Sauye-sauyen da ke cikin sabuwar dokar haraji

Spread the love

*Tinubu ya rattaɓa hannu jiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu akan sababbin dokokin haraji guda huɗu, waɗanda suka tsallake karatu a Majalisar Dokoki na ƙasa a baya.

Shugaban ƙasar ya yi haka ne a Fadar Shugaban ƙasa dake Abuja, inda aka samu halarcin jagorancin majalisa da wasu ‘yan majalisu da gwamnoni da ministoci da mataimakan Shugaban ƙasa.

ƙudirorin sun haɗa da na haraji na ƙasa, na tattara haraji na ƙasa, na samar da hukumar kuɗaɗen haraji da kuma na samar da hukumar haɗaka ta haraji, waɗanda aka tantance su a Majalisar Dokoki ta ƙasa biyo bayan nazari mai zurfi da shawartar masu ruwa da tsaki.

Ana sa ran hakan zai taimaka wajen sauya tsarin tattara haraji a Nijeriya wajen samun ƙarin kuɗaɗen shiga da bunƙasa zuba jari a ciki da wajen Nijeriya.

Awanni kaɗan kafin sanya hannu kan dokokin harajin, Tinubu ya bayyana a shafinsa na Facebook cewa, “tsawon lokaci tsarin harajinmu ya kasance mai wahala da ƙarancin adalci da ya haifar da nauyi ga talakawa. Wannan yanayi ya ƙare yau.”

A cewar shugaban, sabbin dokokin harajin za su taimaka wajen rage nauyin da ke kan ‘yan ƙasa, musamman masu ƙaramin ƙarfi, ƙananan ‘yan kasuwa, da kuma iyalai masu ƙoƙarin tsira da rayuwa.

“Ba kawai dokar rage haraji ba ce, amma sabon alƙawari ne tsakanina da ‘yan Nijeriya. Muna sauƙaƙawa, muna gyarawa, kuma muna haɓakawa,” inji shi.

Shugaban ya yaba wa kwamitin gyaran haraji na Shugaban ƙasa, Majalisar Dokoki, da gwamnonin jihohi bisa rawar da suka taka wajen kammala waɗannan dokoki.

A jawabinsa ga manema labarai, Shugaban Hukumar Tara Haraji ta ƙasa (FIRS), Zacch Adedeji, ya ce dokar tsarin harajin za ta fara ne daga ranar 1 ga watan Janairu, 2026.

Ya ce, “Ya dauki lokaci kafin duk masu ruwa da tsaki, mahalarta, da masu gudanar da ayyukan su canza tsarin.

“Saboda haka, tare da girman majalisar ƙasa, maigirma Shugaban ƙasa ya amince da ƙudirin. Don haka, ranar da zai fara aiki zai kasance 1 ga Janairu, 2026. Muna da cikakkun watanni shida don wayar da kan jama’a da tsarawa. Wannan kuma yana la’akari da shekarar kasafin kuɗi na gwamnati saboda idan kuna da irin wannan canji, ba abin da kuke yi a kafafen yaɗa labarai ba.”

Me sabon ƙudirin ya ƙunsa?

ƙudurin harajin VAT ya ƙunshi sauya yadda ake raba harajin ta yadda za a rage kason gwamnatin tarayya daga kashi 15 cikin 100 zuwa kashi 10 cikin 100, sai gwamnatocin jihohi su samu kashi 55, yayin da ƙananan hukumomi za su samu kashi 35 cikin 100.

Sannan kuma ƙudurin ya zo da sabon fasalin yadda za a kasafta kuɗin harajin tsakanin jihar da ta mallaki kamfani, da kuma inda kamfanonin ke aiki.

ƙudirin ya kuma yi tanadin cewa kamfanonin da ke karɓar VAT za su riƙa kai harajin jihar da shalkwatarsu take maimakon jihohin da rassan kamfanin ke aiki.

Haka kuma ƙudurin ya yi tanadin cewa za a ci gaba da ƙara harajin VAT ɗin har nan da 2030, inda ya yi tanadin cewa za a riƙa ƙara shi zuwa kashi 10 da kashi 12 har daga baya ya koma kashi 15 cikin 100 zuwa 2030.

Wasu daga cikin manyan tanade-tanade da ke ƙunshe a cikin ƙudirin dokar harajin Nijeriya wanda ya yi tasiri a kan ɗaiɗaikun mutane da ‘yan kasuwa sun haɗa da:

Daidaita harajin ilimi kashi 2.5%, harajin NITDA 1% da harajin NASENI 0.25% wanda kamfanoni da yawa ke biya baya ga harajin samun kuɗin shiga na kamfani a duk shekara zuwa harajin ci gaba guda 2% wanda za a yi amfani da shi na musamman don ba da bashin ɗalibai daga shekara ta 2030. 

Wannan yana ƙara rage yawan nauyin haraji na wasu kamfanoni daga kusan kashi 33.75% na abin da suke samu (lokacin da kuka haɗa waɗannan ragi guda uku zuwa adadin harajin kuɗin shiga na su na kashi30%) zuwa kawai kashi 27% na abin da suke samu.

Bitar tsarin raba kuɗaɗen shiga na VAT inda a yanzu jihohi ke karɓar kashi 55% na kuɗaɗen shiga maimakon kashi 50% yayin da kaso na gwamnatin tarayya ya ragu daga kashi 15% zuwa 10%. Kason ƙananan hukumomin ya kasance iri ɗaya.

Ci gaba da haɓaka ƙimar VAT daga 7.5% na yanzu zuwa 10% a cikin shekara ta 2025; 12.5% ​​tsakanin shekarar 2026-2029 da 15% daga 2030.

Keɓance yawancin kayan amfanin yau da kullum da talakawa ke cinyewa daga harajin VAT kamar kayan abinci, harkar lafiya da magunguna, kuɗin ilimi, wutar lantarki da sauransu.

A ɗaya ɓangaren kuma, dokar hukumar haraji ta Nijeriya, ita ce ƙudirin dokar da ta bayyana yadda hukumomin haraji za su gudanar da haraji, waɗanda suka haɗa da tantancewa, tarawa da kuma ƙididdigar kuɗaɗen harajin da suke karɓa. ƙudirin ya kuma zayyana iko da ayyukan hukumomin haraji, harajin da aka keɓe shi kaɗai domin hukumar NRS za ta karɓa da kuma wacce aka keɓe wa jahohi a cikin wasu tsare-tsare daban-daban da suka shafi ingantaccen tsarin haraji a Nijeriya.

A baya ƙudirin ya haddasa cece-kuce:

A wani taro da gwamnonin arewacin ƙasar suka yi a Kaduna, sun ce sabon ƙudirin ya saɓa wa muradun jihohin arewacin ƙasar, inda suka yi kira ga ‘yan majalisar yankin su yi watsi da shi a zauren majalisar dokokin ƙasar.

“Abin da ya sa ba mu yarda ba, shi ne saboda ana karɓar harajin VAT ne a hedikwatar kamfanonin, maimakon inda sauran rassan kamfanonin ke gudanar da ayyukansu ko sayar da kayayyakinsu,” inji shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa, Muhammad Inuwa Yahaya.

”Don haka ne ƙungiyarmu ta yi watsi da wannan sabon ƙudiri, kuma muke kira ga ‘yan majalisar dokokinmu su yi watsi da shi saboda babu abin da ya ƙunsa ban da cutar da al’ummarmu” a cewar gwamnan na Gombe.

A nasa ɓangare shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan sauye-sauyen harajin, Taiwo Oyedele, ya ce kwamitinsu ya ji koken gwamnonin dangane da rashin daidaito da ke cikin sabon ƙudirin rabon harajin na VAT.

Sai dai ya ce manufar sabon ƙudirin shugaban ƙasar ita ce “ɓullo da tsarin da ya dace ta hanyar la’akari da wurin da ake samar da kayayyakin da kuma inda ake sayar da su, da kuma la’akari da jihohin da ke samar da muhimman kayayyaki ko da kuwa ba a biya musu harajin VAT”.

Ya ce: ”Misali, jihar da ke samar da abinci bai kamata ta yi hasara ba saboda kayayyakinta ba su da harajin VAT, amma ana amfani da su a wasu jihohin.

“Yana da kyau a yi la’akari da irin gudunmowar da kowace jiha ke bai wa ƙasar. Haka kuma kamfanonin sadarwa ma za a yi la’akari da wurin da masu amfani da layukan suke.

”Za mu yi aiki da masu ruwa da tsaki don magance wannan damuwa da nufin samun mafita, ta yadda zai yi wa kowane ɓangare daɗi.”

Haka kuma ƙungiyar Ulama ta ƙasa mai shalkwata a garin Kano ta fitar da sanarwar neman a sake nazari a kan shirion yi wa dokar haraji kwaskwarima. Takardar sanarwa da aka buga a wasu manyan jaridun ƙasar nan tare da sa hannun shugaban tafiyar Alhaji Aminu Inuwa Muhammad da sakatarensa Injiniya Basheer Adamu Aliyu tare da kuma wasu manyan malamai 25 daga jihohin arewacin Nijeriya. A sanarwsa sun nemi a sake nazari tare da tattaunawa domin a tafi da kowa da kowa a maganar yi wa dokar harajin kwaskwarima dmin kada a yi kitso da kwarkwarta.

By ukarofi