Kotu a Nasarawa ta yanke wa wanda ya kashe ƴar hidimar ƙasa hukuncin rataya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis ne Babbar Kotun Jihar Nasarawa dake Lafiya ta yanke wa wani Oluwatimileyin Ajayi hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kashe budurwarsa mai suna Salome Adaidu.

Rahotanni sum bayyana cewa, mai laifin ya kashe Salome ne, wadda ƴar hidimar ƙasa ce ta NYSC, da kuma yi wa gangar jikinta gunduwa-gunduwa.

A yayin hukunci game da lamarin, Alƙali Simeon Aboki ya ce an samu Ajayi da laifin kashe ƴar hidimar ƙasar da kuma daddatsa sassan jikinta, lamarin da ya sa aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataye shi.

A lokacin da ya ke magana game da hukuncin, Lauya mai kare Ajayi, Umaru Yunisah ya ce ya yi iya bakin ƙoƙarinsa wajen bai wa mai laifin kariya, saidai haƙarsa ba ta cimma ruwa ba.

Ya ce, yanzu abinda ya rage shi ne mai laifin da iyalansa su ɗaukaka ƙara.

A nasa ɓangaren, lauyan da ke kare masu shigar da ƙara, Raymond Umaru, ya yaba wa korin bisa ƙoƙarinta na tabbatar da gaskiya da adalci.

Ya kuma ce, matuƙar ba su yi hakan a lokacin da ya dace ba, Ma’aikatar Shari’a za ta nemi gwamnan jihar, Abdullahi Sule ya sanya hannu kan hukuncin.

By Babaji