*Yadda aka yi tururuwar jana’iza da ta’aziyyarsa
*Wane ne Muhammadu Buhari
*Yadda Buhari ya gudanar da rayuwarsa a gida
*Fitattun kalamai bakwai da za a riƙa tunawa da Buhari a lokacin mulkinsa
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Bayan duk wasu jita-jita da aka dinga yaɗawa na ƙarya na bayyana rasuwarsa, a ƙarshe dai tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya rasu a wani asibiti da ke Landan bayan ya sha fama da jinya.
A wancan makon ne dai aka yi ta raɗe-raɗin cewa, tsohon shugaba Buhari ya rasu, kamar dai yadda ya faru a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2019, a daidai lokacin da ya ke ganiyar rashin lafiyarsa da ta tilasta masa bai wa mataimakinsa, Osinbanjo, riƙon ƙwarya a lokuta daban-daban, don tafiya ƙasar Burtaniya kula da lafiyarsa.
Sai dai a ƙarshe lokaci ya yi, Muhammadu Buhari ya rasu ranar Lahadi da ƙarfe 4:30 na yamma.
An zaɓi Buhari sau biyu a matsayin shugaban ƙasar Nijeriya a shekarar 2015 da 2023, sannan kuma ya zama shugaban mulkin soja tsakanin Janairu 1984 da Agusta 1985.
Shugabanni da dattawan ƙasa sun yi ta’aziyyar Buhari
Tinubu
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana mutuwar Buhari a matsayin babban rashi ga Nijeriya.
A cikin sanarwar da ya fitar, Shugaba Tinubu, ya bayyana Buhari a matsayin gwarzo, soja, kuma shugaban da ya sadaukar da rayuwarsa wajen gina haɗin kan ƙasa.
“Buhari ya kasance gwarzon ɗan ƙasa da ya shugabanci Nijeriya da cikakkiyar sadaukarwa. Daga mulkin soja a shekarar 1984 zuwa shugabancin dimokuraɗiyya daga 2015 zuwa 2023, ya tabbatar da kishin ƙasa da gaskiya,” inji Shugaba Tinubu.

IBB
Tsohon shugaban mulkin soji a Nijeriya Janar Ibrahim Babangida ya miƙa ta’aziyarsa bisa rasuwar tsohon shugaban ƙasar, Muhammadu Buhari inda ya bayyana shi da mutum mai kyawawan halaye, kuma mai kishin ƙasa.
IBB wanda ya hamɓarar da Buhari daga mulkin soji a ranar 27 ga watan Agustan 1985, ya bayyana shi a matsayin mutumin da ko bayan barinsa mulki, ya cigaba da kasancewa abin koyi ga mutane da dama kuma abin misali.
Ya kuma tuna lokacin da ya fara haɗuwa da Marigayi Buhari a shekarar 1962 a lokacin da suka shiga makarantar horar da sojoji da ke Kaduna.
“Tun a lokacin Muhammadu Buhari mutum ne na daban, bai cika magana ba, amma yana da jajircewa, kuma mutum ne mai bin ƙa’ida kuma mai sauƙin kai, mai tsananin kishin ƙasa ne da sadaukar da kai ga Nijeriya. A cikin shekarun, mun kasance tare cikin wahala da daɗi da jarabawa da kuma cin nasara da rashinsa.”
Babangida ya ce duk da shi da Buhari sukan saɓa kan wasu abubuwa, kamar yadda a kan samu tsakanin ‘yan uwa, “amma ko kaɗan ban taɓa kokwanto game da gaskiyarsa da kishin ƙasa ba.
”Bayan aiki kuma na san shi a matsayin mutum mai addini wanda kuma ke tafiyar da rayuwarsa cikin tawali’u,” inji tsohon shugaban mulkin sojin.
Osinbajo
Mataimakin shugaban Nijeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya miƙa ta’aziyyarsa bisa rasuwar tsohon maigidansa, Muhammadu Buhari.
Osinbajo ya kasance abokin takarar Buhari a zaɓukan shugaban ƙasa na 2015 da 2019, kuma ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban ƙasa tare da Buhari na shekara takwas.
A saƙon ta’aziyyar da ya aike, tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya wallafa cewa : ”Ni da mai ɗakina Dolapo mun sami labarin rasuwar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da rana”
Ya kuma ce ya yi magana da Aisha Buhari, matar tsohon shugaban ƙasar, da kuma ɗansa Yusuf Buhari domin miƙa ta’aziyyarsa da kuma taya su alhinin rashinsa, wanda a cewarsa yana alfahari da aiki tare da shi na tsawon shekara 8 da ba zai taɓa mantawa da su ba.
Mista Osinbajo ya ce Nijeriya ta yi asarar mai kishin ƙasa na asali, wanda rayuwarsa ta kasance cike da ayyukan da ke nuna sadaukarwa ga ƙasarsa da yake ƙauna.
”Tarihin Buhari zai bayar da shaida game da martaba aikin gwamnati da ke cike da gaskiya, da kuma sadaukarwa ga cigaban alumma,” inji tsohon mataimakin shugaban ƙasar.
Atiku
Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya bayyana mutuwar Buhari a matsayin babban rashi da zai bar giɓi a tarihin ƙasar nan.
“Buhari bai kasance shugaban ƙasa kawai ba, ya kasance abin kafa misali wajen ɗa’a, ƙwazo, da son ƙasa. Rayuwarsa ta kasance darasi ga kowane ɗan Nijeriya,” inji Atiku.
Peter Obi
Shi ma Peter Obi, ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai mutunci, wanda ya yi shugabanci da ƙima da ƙwazo.
Ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan Buhari, musamman Hajiya Aisha Buhari da ’ya’yansa, tare da yin addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.
“Ya Ubangiji, ka gafarta masa, ka karɓe shi cikin rahamarka, ka sanya shi cikin Aljannah Firdausi,” inji Obi.
Obasanjo
Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya ce Buhari ya rasu a lokaci da Nijeriya ta fi buƙatar gogewar tsofaffin shugabanni domin fuskantar matsalolin da ke addabar ƙasar.
“Buhari ya taka rawar gani a matsayinsa na soja, shugaba, kuma dattijo. Mutuwarsa rashi ne da yi wa ƙasar nan giɓi,” a cewarsa.
Jonathan
Tsohon Shugaban ƙasa Dr. Goodluck Ebele ya nuna kaɗuwarsa kan rasuwar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.
A cikin wata sanarwa da ya fitar mai cike da alhini da jimami, Jonathan ya miƙa ta’aziyya bisa wannan babban rashi da Nijeriya ta yi ga iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki da kuma gwamnatin Nijeriya.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na sada zumunta Goodluck Jonathan ya bayyana cewa ya karɓi labarin rasuwar tsohon Shugaba Muhammadu Buhari da zuciya mai cike da baƙin ciki da kuma jin rashin mai kishin Nijeriya.
Ya ce Marigayi Buhari ya kasance jagora nagari, ɗan ƙasa mai kishin ƙasa, kuma dattijo wanda ya yi wa Nijeriya hidima a matsayin Shugaban Soja da kuma farar hula inda ya bada gudunmawa fiye da kima wajen wanzar da zaman lafiya da ci gaban ƙasa.
Dr. Jonathan ya bayyana Buhari a matsayin shugaba mai ƙarfin hali, sannan soja mai bin doka da oda, sannan shugaba mai gaskiya da riƙon amana.
Jonathan ya ce Nijeriya ta yi babban rashi, shi kuwa ya rasa abokin aiki kuma dattijo mai daraja.
Jonathan ya ce masu mutunta gaskiya da adalaci ne kaɗai za su jima suna kewar Marigayi Buhari a Nijeriya.
A ƙarshe, tsohon shugaban ya miƙa ta’aziyya a madadin iyalinsa da kuma Gidauniyar Goodluck Jonathan ga iyalan marigayin, da mutanen Jihar Katsina, da ɗaukacin ’yan Nijeriya, tare da addu’ar Allah ya gafarta masa, ya karɓi ayyukan alkhairansa, kuma ya saka masa da Aljannatul Firdaus.
Kwankwaso
Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana alhininsa na rasu Muhammadu Buhari.
“Ina miƙa ta’aziyyata ga iyalansa da kuma Gwamnatin Jihar Katsina da kuma Nijeriya baki ɗaya.
“Ina addu’ar Allah Ya jiƙansa da rahama.”
Wane ne Muhammadu Buhari
An haifi Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Disambar shekarar 1942, a garin Daura da ke jihar Katsina. Muhammadu Buhari shi ne ɗa na 23 a wajen mahaifinsa Malam Harɗo Adamu wanda ya rasu lokacin da Buharin yake ɗan shekara huɗu.
Buhari ya rayu da ‘ya’ya 10 daga matansa guda biyu, Safinatu Yusuf wadda suka rabu a baya da kuma Aisha Halilu wadda aka fi sani da Aisha Buhari wadda ita ce take yi masa takaba.
Muhammadu Buhari ya halarci makarantar allo sannan ya yi kiwon shanu, kafin ya shiga makarantar firamare a garin Daura da Mai’Adua inda ya kammala a 1953.
Daga nan kuma marigayin ya tafi zuwa makarantar sakandare ta Katsina Provisional Secondary School daga 1956 zuwa 1961.
A shekarar 1962 ne Muhammadu Buhari ya shiga aikin soja yana ɗan shekara 19 da haihuwa, inda ya kasance ɗaya daga cikin matasa 70 da aka ɗauka zuwa kwalejin horon sojoji ta Nigerian Military Training wadda daga baya aka sauya mata suna zuwa Nigerian Defence Academy, a 1964.
Haka kuma ya halarci wani kwas na ƙananan sojoji a kwalejin Aldershot da ke Burtaniya daga 1962 zuwa 1963. Kuma a watan Janairun 1963 ne ya samu matsayin Second Lieutenant kuma ya jagorancin rundunar sojin ƙasa ta Second Infantry Battalion da ke Abeokuta.
Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin da ya hamɓarar da Janar Aguiyi Ironsi, inda aka maye gurbinsa da Janar Yakubu Gawon, a 1966.
Daga bisani kuma aka naɗa shi shugaban hukumar NNPC wadda aka fara kafawa a shekarar 1977.
Manjo Janar Muhammadu Buhari ya taka rawar gani a juyin mulkin shekarar 1983 da ya yi sanadiyyar hamɓarar da gwamnatin Alhaji Sehu Aliyu Usman Shagari, inda kuma shi ya zamo shugaban mulkin soja.
To sai dai kuma Manjo Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya yi wa Manjo Janar Buhari juyin mulki a watan Agustan 1985, inda kuma aka tsare shi har zuwa shekarar 1988.
Tauraruwar Buhari ta fara haskawa a lokacin da aka ba shi muƙamin ministan man fetur da ma’adanai a shekarar 1975, a zamanin mulkin sojin janar Obasanjo.
A zamanin mulkin Janar Sani Abacha an nada Buhari shugaban hukumar PTF wadda aka kafa da kuɗaɗen rarar man da ƙasar ta samu a wannan lokaci domin gudanar da ayyukan ci gaban al’umma.
Kuma ayyukan da Buhari ya yi wa Nijeriya kama daga hanyoyi, asibitoci zuwa makarantu ya sa wasu ‘yan Nijeriya son ganin ya sake zama shugaban ƙasar.
Ko da yake kafin nan shi ne gwamnan sabuwar Jihar Arewa maso Gabas da Janar Murtala Ramat Muhammed ya ƙirƙiro.
Sau biyu Muhammdu Buhari yana tsayawa takarar shugaban ƙasa ƙarƙashin tutar jam’iyyar ANPP a 2003 da 2007, waɗanda duka bai samu nasara ba.
Rashin nasarar da ya yi karo biyu bai sauya masa ra’ayi game da siyasar Nijeriya ba, kuma ya ƙaddamar da tashi jam’iyyar da ya kira CPC wadda a ciki ya sake tsayawa takarar shugaban ƙasa a zaɓen da aka yi a shekarar 2011.
Sakamakon cimma haɗakar jam’iyyu da aka sanya wa suna APC, Muhammadu Buhari ya samu nasarar lashe zaɓen shekarar 2015, inda ya kayar da abokin takararsa, Goodluck Jonathan na jam’iyyar PDP mai mulki.
Muhammadu Buhari ya sake samun damar yin tazarce a karo na biyu a 2019, bayan kayar da abokin takararsa, Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP.
Buhari ya kammala wa’adinsa na biyu a ranar 29 ga watan Mayun 2023, bayan samun nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Daga nan ne kuma Buhari ya koma mahaifarsa ta Daura inda bayan kimanin shekara guda sai ya koma birnin Kaduna ya ci gaba da zama.
Shugaba Buhari ya shafe tsawon lokaci yana jinya a shekarar 2017, inda har ya shafe sama da kwana 100 yana jinya a Birtaniya.
Wannan al’amari ya jawo ce-ce-ku-ce sosai a ciki da wajen ƙasar.
A lokacin da ruɗani ya yawaita kan halin da shugaban ke ciki da kuma rashin jin ta bakin makusantansa game da ainihin abin da ke damun shugaban.
An kwantar da ɗan uwa kuma na hannun daman Buhari, Mamman Daura a asibiti a Landan
Mamman Daura, ɗan uwa ga Marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, yana fama da rashin lafiya kuma an kwantar da shi a wani asibiti da ke Landan, inda ya ke samun sauƙi, inji wani jami’in gwamnati.
Ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya tabbatar da rashin lafiyar Mamman Daura a cikin wata sanarwa yayin da ya ke bayani kan tafiyar Mataimakin Shugaban ƙasa zuwa Landan.
Manhaja ta ruwaito cewa Shettima, bisa umarnin Shugaba Bola Tinubu, shi ne ya jagoranci tawagar Nijeriya zuwa Landan domin ɗauko gawar Buhari zuwa Nijeriya.
“A madadin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima, da isarsa Landan, ya gana da iyalan marigayi tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Landan don yi musu ta’aziyya.
“Mataimakin Shugaban ƙasa ya kuma ziyarci ɗan uwan marigayin, Malam Mamman Daura, wanda ke samun sauƙi a wani asibiti a Landan,” inji sanarwar da ofishin Mataimakin Shugaban ƙasa ya fitar ta bakin mai magana da yawunsa, Stanley Nkwocha.
Yadda Buhari ya gudanar da rayuwarsa a gida
Kamar kowanne ɗan adam, shi ma yana da tsarin yadda yake gudanar da rayuwarsa a kullu-yaumin, daga fitowar rana zuwa faɗuwarta.
Tsohon ministan jiragen sama na Nijeriya a zamanin mulkin Buharin, wanda kuma ke da alaƙa ta ut da ƙut da shi, da kuma iyalinsa, ya bayyana wa BBC yadda tsohon shugaban ƙasar ke gudanar da harkkin rayuwarsa daga asuba zuwa kwanciya barci.
Hadi Sirika ya bayyana marigayin da mai ɗimbin imani, wanda a cewarsa ke mutunta rayuwar ɗan’adam da ta dabbobi da sauran halittun Allah.
Ya ƙara da cewa mutum ne mai tausayi da gaskiya da riƙon amana tare da kyautatawa.
”Marigayin mutum ne da ba ya son wulaƙanta ɗan’adam da duka halittun Ubangiji, musamman dabbobin da yake kiwonsu,” inji shi.
Mutum ne mai haƙuri da kula da dangi, ”baya son ganin an wulaƙanta duk wani abu mai rai,” inji Hadi Sirika.
Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar kan tashi daga barci, tun kafin ketowar asuba, sannan ya kammala shirin zuwa masallaci domin yin sallar jam’i.
”Bayan kammala sallar asuba yakan zauna ya yi azkar daidai gwargwado kafin ya koma gidansa, kuma ba ya komawa barci.”
Idan lokacin da yaransa ke zuwa makaranta ne zai tabbatar da yaransa sun tashi domin su tafi makaranta a kan lokaci, a cewar Hadi Sirika.
”Bayan hakan yakan zagaya gidansa kaf, domin ya ga yadda kowa ya tashi a gidan,” inji Hadi Sirika.
Hadi Sirika ya ce bayan kammala duk waɗancan hidimomi, tsohon shugaban ƙasar kan zauna domin sauraron radiyo, mutum ne son sauraren radiyo, musamman BBC Hausa.
”Bana tsamanin akwai shirin BBC Hausa da yake wuce shi, zai kunna ya saurari duka shirin BBC,” inji tsohon Ministan.
Hadi Sirika ya ce a irin sauraron BBC Hausa da yake yi ne, wata rana ya ji musayar kalamai da tsohon ministan ya yi da wani.
”Nan take ya kirawoni ya ce me ya sa kuke musayar kamalamai da wane, rashin fahimtar juna ne ya sa abin naku ya kai haka,” inji shi.
Makusancin Buharin ya ce tsohon shugaban ƙasar mutum ne da ya gina kyakkyawar alaƙa da iyalansa.
”Duk da cewa ba zan iya cewa komai game da rayuwar matarsa ta farko ba, amma dai ga ‘ya’yansa mutum ne mai kyakkyawar alaƙa da su.
”Rayuwar da yake yi da ‘ya’yansa rayuwa ce ta barkwanci da wasa da dariya da tsausayawa da kuma ƙaunar juna.
”Idan ka ga yadda yake rayuwar barkwanci da ‘ya’yansa sai ka ɗauka jikokinsa ne ba ‘ya’ya ba,” inji Hadi Sirika.
Yakan zauna da iyalansa su ci abinci tare su yi raha su yi barkwanci, a cewar Sirika.
Tsohon Ministan ya ce a mafi yawan lokuta idan sun zauna da marigayin kana yawaita yi musu nasiha da riƙon amana.
”Idan aiki aka ba ka to ka riƙe amana, domin ai shugaban ƙasa na shi ne kaɗai ke mulkin ƙasar bap.
”Yana yawan yin magana game da yadda tsarin mulki yake, (kowane mai muƙami yana da rawar da zai taka),” inji shi.
Makusancin Buharin ya ce abinci da tsohon shugaban ƙasar ya fi so shi ne tuwon alkama miyar kuka da kuma ganye kamar salat.
Ya kuma ce marigayin ma’abucin son shan shayi ne, da bai fiya cin abinci da yawa ba.
”Yana da saurin jin yunwa, amma kuma ba ya cin abinci da yawa, da ya ci kaɗan sai ya ƙoshi,” inji shi.
Hadi Sirika ya ce Buhari mutum ne mai son tsirrai da dabbobi.
Ya kuma ce mutum ne mai son zuwa gonarsa, musamman ya ga dabbobinsa da yake kiwonsu.
”Shi duk inda ya zauna sai ya shuka itatuwa, ya yi lambu, ya zauna tare da su,” inji shi.
Ya ƙara da cewa marigayin mutum ne mai son motsa jiki da yawa.
Fitattun kalamai bakwai da za a dinga tunawa da Buhari a lokacin mulkinsa
1. “Ni na kowa ne kuma ni ba na kowa ba ne”
Wannan na ɗaya daga cikin kalaman da Buhari ya yi amfani da su, a lokacin da yake jawabi a bikin rantsar da shi a shekarar 2015. Ya bai wa mutane tabbacin cewa zai yi mulki cikin adalci ba tare da fifita wasu akan wasu ba.
2. “Idan Nijeriya ba ta kashe rashawa ba, cin hanci da rashawa zai kashe Nijeriya.”
Wannan magana ta zama babban take a zamanin Buhari. Hakan ya nuna irin yadda ya yi da gaske game da yaƙi da cin hanci da rashawa, duk da cewa daga baya da yawa sun yi zargin cewa yaƙin ya kasance bai yi nasara ba.
3. “Ba ni da gida a ƙasar waje, idan ina da shi, ku je ku ƙwace.”
Buhari ya faɗi haka ne domin ya tabbatar da cewa ya yi rayuwa mai sauƙi kuma bai yi sata a ƙasar ba. Ya yi hakan ne domin nuna gaskiya, duk da cewa wasu ‘yan Nijeriya na shakkar hakan.
4. “Duniya ta canza, kuma dole ne mu canza a yadda ta zo”
Wannan magana ta zo ne a lokacin ɗaya daga cikin jawabinsa na ciyar da Nijeriya gaba. Buhari ya yi amfani da shi wajen faɗawa ‘yan Nijeriya cewa canji ya zama dole, kuma gwamnatinsa a shirye take ta jagoranci wannan canjin.
5. “Matasan Nijeriya malalata ne, cima zaune”
Wannan magana ta haifar da cece-kuce musamman a tsakanin matasa. Buhari ya faɗi haka ne a wata zantawa da ya yi a ƙasar waje, kuma da dama na ganin hakan cin fuska ne. Ya yi ta yawo a kafafen sada zumunta na tsawon kwanaki tare da saka hashtags kamar #LazyNigerianYouths.
6. “Ayyukan da jaruman mu suka yi a baya ba za su taɓa tafiya a banza ba”
Duk da cewa yana daga cikin taken ƙasar, Buhari ya sha maimaita wannan layi don tunatar da mutane irin sadaukarwar da shugabanni da sojoji suka yi. Ya yi amfani da ita wajen inganta haɗin kai da kishin ƙasa.
7. “Zan ci gaba da yaƙi domin talakawa.”
Wannan magana tana cikin yawancin jawaban Buhari. A kullum ya ce yana so ya rage raɗaɗin talauci da taimakon talakawan Nijeriya musamman na Arewa. Ko an cimma wannan buri ya kasance muhawara.
