Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse
Shugaban ƙaramar hukumar Jahun a Jihar Jigawa Alh Jamilu Ɗan Malam yaja kunnen kansiloli masu gafaka da marasa gafaka su haɗa kai ta fuskar aiki a tsakaninsu domin ganin sun taimaka wajen kawo cigaba a ƙaramar hukumar.
Alhaji Jamilu yayi wannan gargaɗin ne jim kaɗan bayan ƙaddamar da kansiloli masu gafaka da marasa gafaka da Kuma masu bashi shawara a ofishinsa a ranar Talatar da ta gabata.
Da yake ƙaddamar da tawagar kansilolin da masu bashi shawara a ofishinsa ya hore su da su zauna lafiya da juna kuma su kiyaye doka da ta hana wani ya riƙa shiga aikin wani saboda kaucewa samun saɓani a tsakaninsu.
Ya kuma horesu da su zama masu haƙuri da juna tare da riƙe sirrin gwamnati a duk lokacin da ƙaramar hukumar tayi zama da su.
Ya kuma hore su da su zama masu biyayya ga shugabanci, Kuma kowa ya tsaya akan aikin da ƙaramar hukumar ta ɗora shi.
Daga cikin waɗanda shugaban ƙaramar hukumar ya ƙaddamar akwai kansiloli 10 masu gafaka da Kuma goma marasa gafaka da kuma masu bashi shawara a fanni daban daban mutum bakwai.
Kuma dukkan kansilolin masu gafakar 10 nan take shugaban ƙaramar hukumar ya basu ofisoshin su da za su gudanar da ayyukansu domin cigaban ƙaramar hukumar ta Jahun.
Ya ƙara da cewar daga cikin kansilolin 27 kawai za su sami damar shiga zauren majalissar a lokacin zaman majalissar ƙaramar hukumar.
