Ranar 22 ga Yuli kamfanin Blueprint zai gudanar da gagarumin bikin bada lambobin yabo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Dukkan shirye-shirye sun kai ga matakin ƙarshe na gudanar da babban taron shekara-shekara na bikin bayar da lambobin yabo na Kamfanin Jaridun Blueprint, wanda za a gudanar a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025, a otel ɗin Abuja Continental Hotel (tsohon Sheraton otel) da misalin ƙarfe 9:30 na safe.

Taron, wanda zai zama wani dandali ne na yin tambayoyi da tattaunawa game da harkokin mulki, zai kuma zama dandalin tofa albarkacin baki kan matsalolin ƙasa da ka iya yin tasiri ga rayuwar al’umma.

Haka zalika, taron na neman a san shugabannin da suka fi hidimta wa jama’a da kuma na bangaren kamfanoni masu zaman kansu, da suka haɗa da fitattun mutane da ke kawo sauyi a rayuwar al’umma.

Manajan Daraktan Jaridun Blueprint, Malam Salisu Umar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata a Abuja.

Ya ce: “Kamfanin Jaridun Blueprint na farin cikin sanar da cewa za a gudanar da bikin bayar da lambar yabo ta 2024 a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2025, a otel ɗin Abuja Continental (tsohon Sheraton otel), daga misalin ƙarfe 9:30 na safe.

“Taron, wanda zai zama wani dandali na karrama shugabanni nagari a harkokin mulki, tsayuwar siyasa, da kuma tasirin kawo sauyi a sassan gwamnati da kamfanoni masu zaman kansu na Nijeriya, za a gabatar da wani muhimmin lacca mai gamsarwa da Farfesa Attahiru Jega, mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan shirin sake fasalin kiwon dabbobi zai gabatar,” inji shi.

Salisu ya ce: “Farfesa Jega zai yi magana a kan maudu’in binciko hanyoyin ci gaban kiwon dabbobi a Nujeriya,” batun da aka zaɓa cikin tsanaki don nuna fifikon ƙasa a halin yanzu dangane da haɓaka tattalin arziki da samar da abinci.

Taken bikin wannan shekara ya yi daidai da lokacin da Nijeriya ke ƙoƙarin sake mayar da ɓangaren kiwonta a matsayin ginshiƙin kawo sauye-sauye a masana’antu, samar da ayyukan yi da hada-hadar kasuwanci a duniya. Kiwon dabbobi ya kasance ɗaya daga cikin ginshiƙan ci gaban tattalin arzikinmu. Babban jawabin da Farfesa Jega zai yi zai samar da ƙarin haske kan yadda Nijeriya za ta iya dawo da martabar ci gaban ƙasa zuwa ƙasashen waje.

“Bikin na 2024 zai haɗa manyan mutane a duk faɗin shugabanci, masana’antu, ci gaba, tsaro, kafofin watsa labarai, da diflomasiyya. Baƙin da ake sa ran za su halarta sun haɗa da masu gwamnoni masu ci da tsoffi, ministoci, shugabannin manyan cibiyoyi, shugabannin hukumomi, manyan jami’an diflomasiyya, shugabannin kamfanoni da abokan ci gaba.

Har ila yau, taron zai gabatar da baje kolin bayar da lambar yabo ga fitattun mutane da cibiyoyi waɗanda suka nuna bajintar da ba a saba gani ba wajen hidimta wa al’umma da samar da ci gaban tattalin arziki.

By ukarofi