Manyan ƙasa sun yi tsokacin shekara biyun Tinubu

Spread the love

A ƙara haƙuri da tsare-tsaren Tinubu – Buhari

Manufofin attajirai ne, ba na talakawa ba – Atiku

Sauye-sauyen kasuwaci abin a yaba ne – BUA

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Kamar yadda aka yi tsammani, yayin da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya cika shekara biyu akan karagar mulki a jiya Alhamis, 29 ga Mayu, 2025, masu ruwa da tsaki sun tofa albarkacin bakinsu kan rawar da gwamnatinsa ta taka a tsawon wannan lokaci. Cikin waɗanda suka yi tsokaci akwai wanda ya gada, tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da jagoran ’yan adawa ƙasar kuma tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar da kuma fitaccen ɗan kasuwa a Nijeriya da Afrika, Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu.

Buhari:

A matsayinsa na wanda bai jima da sauka daga karagar mulki ba, za a iya cewa, ya fi kowa masaniya kan halin da mulkin ƙasar ke ciki a cikin tsofffin shugabannin Nijeriya, Tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya taya Shugaba Bola Tinubu murna yayin da gwamnatinsa ke cika shekaru biyu kan mulki tare da jan hankalin ’yan Nijeriya da su yi haƙuri da sauye-sauyen gwamnatin Tinubu, don cimma buri a nan gaba.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar, Buhari ya buƙaci a ci gaba da goyon bayan gwamnatin APC, yana mai gargaɗi cewa kada a bar matsin lamba na siyasar cikin gida ya hana aiwatar da sauye-sauyen da ake buƙata.

Sanarwar mai taken “Tinubu Ya Samu Yabon Buhari da Shawararsa a bikin cika shekaru biyu” ta bayyana cewa matsalolin da suka haɗa da talauci da hauhawar farashin kaya,  waɗanda suka fi shafar talakawa, gwamnati kaɗai ba za ta iya magance su ba.

Sai dai hakan ya janyo matsanancin hauhawar farashi da tsadar rayuwa a cikin gida.

A ranar 23 ga Mayu, 2025, jam’iyyar APC ta bayyana Tinubu a hukumance a matsayin ɗan takararta guda daya tilo don zaben 2027, duk da fuskantar sauyin ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.

Buhari ya jinjina wa ƙoƙarin Tinubu wajen rage talauci da hauhawar farashin kayayyaki, yana mai kira ga fannoni masu zaman kansu da ɗaukacin ‘yan ƙasa da su ba da gudunmawarsu.

Ya kammala da cewa: “Ina taya Shugaba Tinubu murnar cikar shekaru biyu a ofishi. Allah ya ci gaba da ba ka hikima da tausayi wajen jagoranci. Mu kuma mu rage tsammaninmu daga gwamnati.”

Ya ce yana goyo bayan ƙoƙarin da gwamnatin APC ke yi na rage talauci da tashin farashi, da ya ce sun yi matuƙar shafar rayuwar talakawa.

Tsohon shugaban Nujeriyan ya ƙara da cewa matakan da ake ɗauka na rage talauci da tsadar rayuwa, ba abubuwa ne da ya kamata a bar gwamnati ita kaɗai da yin su ba.

Ya kuma buƙaci ‘yan wasar da kada su karaya a kan makomar Nijeriya

“Ɓangarori masu zaman kansu da dukan mu ‘yan Nijeriya ya zama wajibi mu haɗa hannu domin bayar da gudummuwarmu,” inji tsohon shugaban Nijeriyar, Muhammadu Buhari.

Atiku:

Sai dai kuma babu mamaki ganin yadda jagoran ’yan adawa a Nijeriya kuma ɗan takarar Shugaban ƙasa na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2023, tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar, ya caccaki Gwamnatin Bola Ahmed Tinubu da kakkausar murya, yana mai cewa, cikin shekara biyu kacal, gwamnatin ta nuna gazawa, kuma gwamnati ce wadda ba ta tare da jama’a sannan maras jin tausayin talakawa fiye da kowacce gwamnati tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a Nijeriya.

A wata sanarwa da ya fitar gabanin cikar gwamnatin Tinubu shakaru biyu kan mulki, Atiku ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ba za ta yi shiru ba yayin da halin rayuwa ke ƙara tsananta ga ‘yan ƙasa tare da yawaitar almubazzaranci daga ɓangaren gwamnati.

Atiku ya ce, babu wata gwamnati da ta taɓa jefa al’umma cikin irin wannan ƙunci ba tare da la’akari da gaskiya da riƙon amana da jagoranci nagari ba.

“Wannan gwamnati ta Tinubu ba wai kawai ta ƙara talauci a faɗin ƙasar ba ne, har ma ta kafa sabbin tarihi wajen almubazzaranci da kuɗaɗen jama’a.”

Ya ƙara da cewa, a daidai lokacin da miliyoyin ’yan Nijeriya ke fama da matsin rayuwa, jami’an gwamnati suna rayuwa cikin walwala da amincewa da kasafin kuɗi da ke amfana kawai ga attajirai yayin da talakawa ke ci gaba da shan wahala.

“Abin taƙaici ne yadda Nijeriya ba wai kawai ta kasance ƙasa da ke fama da matsanacin talauci a duniya ba, yanzu haka ta zama ƙasar da ke da yawan yara masu fama da rashin abinci fiye da kowacce ƙasa a Afirka, hatta fiye da Sudan — ƙasar da ke fama da yaƙi,” inji Atiku.

Ya ce bisa rahoton Global Hunger Indeɗ na 2024, Nijeriya na daga cikin ƙasashen da suka fi fama da yunwa da rashin abinci, inda take matsayi na 18 a duniya.

Ya ƙara da cewa, duk wani tsarin gwamnati da aka ɗauka a ƙarƙashin wannan mulki ya fi cutar da talakawa fiye da komai, yayin da masu kuɗi ke ci gaba da morewa.

Atiku ya ce, abin da ya fi tayar da hankali shi ne yawan bashin da gwamnatin ke ci gaba da karɓa.

“A lokacin da Tinubu ya hau mulki a shekarar 2023, jimillar bashin ƙasar ya tsaya kan naira tiriliyan 49. Amma cikin shekaru biyu kacal da fara mulki, ya karu zuwa tiriliyan 144 yayin da kuma ake shirin karɓar ƙarin bashi daga ƙasashen waje wanda zai iya kai bashin ƙasar zuwa tiriliyan 183.”

Atiku ya ce, su a matsayin su na jam’iyyar adawa da masu kishin ƙasa, ba za su zuba ido ba su kalli abubuwan da ke faruwa ba su ci gaba.

BUA:

Shi kuwa shahararren attajiri a Nijeriya da kuma Afrika Shugaban Kamfanin BUA Group, Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, ya kalli yadda Shugaba Tinubu ya gudanar da tsare-tsaren gwamnatinsa ne ta fuskar kasuwanci, inda ya bayyana gamsuwarsa da yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da harkokin tattalin arziki da masana’antu a Nijeriya, yayin da gwamnatin ke cika shekaru biyu a mulki.

A cikin wata takarda da ya fitar mai taken “Shekara Biyu na Shugaba Tinubu: Duba daga babin kasuwanci” Abdulsamad ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar, musamman cire tallafin man fetur da haɗewar tsarin musayar kuɗaɗe (Fɗ), na daga cikin muhimman matakan da suka ceto tattalin arzikin ƙasar daga rugujewa.

A cewarsa, cire tallafin fetur da Shugaba Tinubu ya yi tun ranar farko da ya hau mulki, ya daƙile barnar da ake yi wa tattalin arzikin Nijeriya. Ya ce kafin cire tallafin, kasashe maƙwabta kamar Jamhuriyar Nijar da Benin na cin moriyar fetur ɗin Nijeriya wanda ake sayar da shi a kan kuɗi marasa yawa.

“A lokacin da na ziyarci Jamhuriyar Nijar, Shugaban ƙasar ya ce kaso 100 na fetur da suke amfani da shi daga Najeriya yake fitowa. Hakan yana nuna yadda tallafin man Nijeriya ke amfanar da ƙasashen waje,” inji shi.

Ya ƙara da cewa cire tallafin ya rage shan man fetur da kashi 40 zuwa 50, yana mai jaddada cewa yawan kuɗin da ake samu yanzu ana amfani da su wajen gina ababen more rayuwa da taimakawa jihohi.

Abdulsamad ya kuma bayyana cewa kafin haɗewar tsarin musayar kuɗaɗe, yawancin ‘yan kasuwa sukan kwashe lokaci suna yawo a Babban Bankin Nijeriya (CBN) domin samun dala a farashi na gwamnati. Amma yanzu, sabon tsarin Shugaba Tibubu ya buɗe kuma yana aiki ba tare da matsin lamba ko neman alfarma ba.

“Na haɗu da Gwamnan CBN sau ɗaya cikin shekaru biyu, saɓanin da, inda sai ka kwana a Abuja domin samun dala. Yanzu muna samun dala daga kasuwa cikin sauƙi,” inji shi.

Abdulsamad ya yaba wa gwamnatin Tinubu da kafa daidaito da bin doka cikin harkokin kasuwanci, inda ya bayar da misali da yadda aka rufe wani kamfanin su a Port Harcourt saboda son zuciyar wani babban jami’in gwamnati a baya, amma irin hakan bai sake faruwa da su yanzu ba.

“A yau, babu wanda zai iya tashi ya rufe kamfanin wani don kawai yana goyon bayan abokin gasar sa na kasuwa. Gwamnatin Tinubu ba za ta lamunci hakan ba,” inji shi.

Alhaji Abdulsamad Rabiu ya ce tun daga lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki, kamfaninsu ya zuba sama da dala biliyan ɗaya a Nijeriya, musamman a ɓangaren abinci, makamashi da siminti. Ya ce ƙarin kuɗaɗen shiga da gwamnati ke samu daga cire tallafin mai da haɗewar kasuwar kuɗaɗe, ya ba su damar tsara dogon zango na ci gaba.

Dangane da tsadar kayan abinci, Abdulsamad ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa saukar da haraji kan shigo da shinkafa, wanda ya hana masu ɓoye shinkafa samun sukunin kƙara farashi. Ya ce wannan mataki ya sauƙaƙa wahala kuma ya nuna hangen nesan Shugaba Tinubu. 

A ƙarshe, Alhaji Abdulsamad Rabiu ya bayyana cewa, Nijeriya ta na da komai da ake buƙata: albarkatu, mutane da ƙwararru, kuma yanzu tana da shugabanci mai inganci. Ya buƙaci ‘yan kasuwa da masu zuba jari su yarda da Nijeriya kuma su ci gaba da zuba jari a cikinta.

“Abin da Shugaba Tinubu ya yi shi ne: ya cire tallafin fetur wanda shine mafi girman almundahana a tarihin tattalin arzikinmu. Ya hade kasuwar kuɗaɗe. Ya dawo da daidaito da aminci a kasuwa. Wannan shi ne tubalin ci gaban kasa,” inji shi.

By ukarofi