Neja: Mutane 21 sun rasu yayin da 10 suka ɓata a ambaliyar Mokwa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Wani mamakon ruwan sama da aka yi na tsawon sa’o’i a Ƙaramar Hukumar Mokwa dake Jihar Neja, ya yi sanadiyyar samuwar ambaliyar da ta yi sanadin mutuwar mutane 21, a yayin da wasu sama da 10 kuma suka ɓata.

A wata takarda daga Daraktan riƙon ƙwarya na Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar (NSEMA), Ibrahim Hussaini, lamarin ya shafi yankunan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa ne dake garin Mokwa.

Ambaliyar ta haɗe wurare da dama inda ta mamaye gidaje sama da 50 a yankin da mutanensu, lamarin da ya haifar da rasa rayuka da dukiyoyi tare da raba da dama da muhallansu.

Akan haka ne NSEMA da haɗin-gwiwar hukumar ƙaramar hukumar da masunta da ƴan sa-kai suka ƙaddamar da aikin ceto na gaggawa don tsamo gawawwaki da waɗanda ke jiran ɗauki acikin iftila’in.

A yayin haɗa wannan rahoton, an ruwaito cewa an ceto wata mata da ƴaƴanta biyu, waɗanda aka garzaya da su Babban Asibitin Mokwa domin ba su kulawa.

NSEMA ta kuma ce, har yanzu ana cigaba da ƙoƙarin ceto mutane sama da goman da suka ɓata.

Haka kuma hukumar ta tabbatar wa al’umma cigaba da bada tallafi na kayayyakin agaji ga waɗanda lamarin ya shafa.

By Babaji