SSCE: Majalisar Wakilai ta bai wa WAEC sa’o’i 24 ta bayyana a gabanta bayan ƙin amsa gayyatar farko

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Kwamitin kula da Ilimin matakin farko da Hukumomin jarrabawa na Majalisar Wakilai ya bai wa jagorancin Hukumar kula da jarrabawa a Yammacin Afirka (WAEC) wa’adin kwana ɗaya ya hallara a gabansa, wato a yau Juma’a, 30 ga watan Mayu, 2025, domin warware matsalolin da suka dabaibaye jarrabawar SSCE da ke gudana.

Shugaban kwamitin, Oboku Oforji ya bayyana hakan a ranar Alhamis a sakamakon ƙin amsa irin gayyatar a karon farko.

Ya ce, kwamitin ya gayyaci WAEC ne don ya bada ba’asi game da ƙorafe-ƙorafen da ake samu gami da ayyukan da ba su dace ba da ake yi a yayin jarrabawar.

A baya ne kwamitin ya yi aiken saƙon gayyatar ga hukumar, domin zuwa a ranar 27 ga Mayu na neman ta yi bayani gamsashshe ga al’umma akan matsalolin.

Ya koka kan yadda WAEC ta gaza halarta majalisar a ranar da aka tsara, wato 29 ga watan Mayu, yana mai bayyana hakan a matsayin abinda ba za su lamunta ba duba da yadda ya shafi al’umma kai-tsaye.

Ya kuma ce, matuƙar ta ƙi zuwa a ranar Juma’a, to majalisar za ta yi amfani da ƙarfin doka wajen ɗaukar matakin da ya dace.

By Babaji