Yadda Tinubu ya ceci Ribas wajen sanya dokar ta-ɓaci – Fubara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Sanya dokar ta-ɓaci da Shugaba Bola Tinubu ya yi a Jihar Ribas ya taimaka wajen tsare jihar daga faɗawa cikin halin mulki mara tsari, kamar yadda dakataccen gwamnan jihar, Siminalayi Fubara ya bayyana a ranar Alhamis.

Ya ce, hanzari da Shugaba Tinubu ya yi wajen tsoma baki a siyasar jihar ya tseratar da ita daga fuskantar ƙalubalen rikicin siyasa da aka yi fama da shi a baya.

Ya kuma kirayi magoya bayansa da ƴan Ribas gami da ɗaukacin al’ummar Nijeriya da su yaba wa Tinubu bisa hikima da ya yi amfani da ita a lokacin da ya dace, yana mai cewa zaman lafiya da sulhu gami da dawo da zaɓaɓɓun ƴan siyasa za su dawo a jihar.

Fubara ya tabbatar da cewa demokraďiyya da shugabanci na gari za su koma aiki a jihar nan ba da jimawa ba, yana mai nuna muhimmancin dukkan ɓangarori biyun wajen hidimta wa al’umma.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labaransa, Nelson Chukwudi ya fitar, ya ce Fubara ya bayyana hakan ne a yayin ganawa da masu-ruwa-da-tsaki da jagororin tafiyarsa wadda aka yi da nufin taya shi murnar kammala shekaru biyu a mulki, a Fatakwal.

Kazalika, ya nemi magoya bayan nasa da su kasance masu son neman zaman lafiya domin ciyar da jihar gaba.

Har’ilayau, dakataccen gwamnan ya nemi yafiyar dukkan waɗanda ya saɓa wa a yayin hukunci kan rikicin siyasa a jihar, yana mai cewa ya yi hakan ne don maslahar zaman lafiya da ci-gaban jihar.

Haka kuma ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa da za a samu sasanci a tsakanin sa da wanda ya gada a kujerar mulkin jihar, wanda kuma shi ne ministan Abuja a yanzu, wato Nyesom Wike.

By Babaji