Kuɗin ƙasa: Garƙame gurare ya saɓa doka – Sanata Kingibe ga Wike

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Sanata mai wakiltar Babban Birnin Tarayya Abuja, Sanata Ireti Kingibe, ta ce, ba daidai ba ne a ƙwace ko rufe ko garƙame kadarar kowa, saboda rashin biyan kuɗin ƙasa na shekara-shekara ba.

Yayin da ta ke mayar da martani game da al’amuran da ke faruwa a babban birnin ƙasar, ‘yar majalisar ta gargaɗi ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da ya guji karya doka.

Hukumar kula da babban birnin tarayya, FCTA, a bisa umarnin Wike, ta ƙwace gidaje sama da 4,700, waɗanda aka ce masu su sun kasa biyan kuɗin ƙasa tsawon shekaru da dama.

A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne gwamnatin ta fara rufe kadarorin da abin ya shafa da suka haɗa da Hukumar Tara Haraji ta ƙasa FIRS da sakatariyar jam’iyyar PDP, otel ɗin Ibro da dai sauransu, kafin shugaban aasa Bola Ahmed Tinubu ya shiga tsakani, inda ya baiwa waɗanda suka kasa biyan kuɗin ƙasan wa’adin kwanaki 14.

Sai dai da take mayar da martani kan lamarin, Sanata Kingibe ta ce dokar amfani da filaye ta nuna cewa hukuncin da za a yi wa irin wannan lamari bisa tsarin doka shi ne, cin tara ba wai a kwace ko rufe kadarorin mutane ba ba tare da bin ƙa’idojin da aka shimfiɗa a ƙarƙashin sashe na 42 na dokar amfani da filaye da sauran abubuwan da suka dace ba.

Ta ce, “Waɗannan ayyuka suna lalata rayuwa tare da zubar da kimar gwamnti a idon jama’a.

‘’A matsayina na zaɓaɓɓiyar Sanatan Babban Birnin Tarayya, ba zan zuba ido na tsaya ba yayin da ake muzguna wa al’umma. Ina yin cuɗanya da hukumomin da abin ya shafa tare da binciko duk hanyoyin da za a bi don tabbatar da cewa duk wani matakin aiwatar da doka da aka ɗauka ya yi daidai da tsarin doka, adalci da kuma nuna tausayi, inji ta.

By ukarofi