Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya, Janar Yakubu Gowon, a ranar Laraba, ya ce ƙungiyar ECOWAS ta samo asali ne bayan wata tattaunawa da ya yi da Marigayi Shugaban ƙasar Togo, Janar Gnassingbe Eyadema, bayan yaƙin basasar Nijeriya.
Tsohon shugaban na Nijeriya ya yi magana ne a Legas yayin bikin cika shekaru 50 da kafa ƙungiyar ECOWAS, a cibiyar kula da harkokin ƙasa da ƙasa ta Nijeriya da ke titin Kofo Abayomi.
A daidai wurin ne aka rattaɓa hannu kan yarjejeniyar tarihi da shugabannin ƙasashen yammacin Afirka 15 suka sanya hannu a ranar 28 ga Mayu, 1975.
Gowon mai shekaru 90, wanda shi ne kaɗai a raye daga cikin waɗanda suka kafa ƙungiyar ECOWAS, ya shaida wa mahalarta taron shugabannin Afirka da wasu fitattun mutane, cewa ra’ayin ya samu ne a lokacin da ya kai ziyara a yankin domin godewa ƙasashe bisa goyon baya da fahimtar da suka yi a lokacin yaƙin basasar Nijeriya.
Ya ce: “Wannan ra’ayin ya fara ne jim kaɗan bayan yaƙin basasa, lokacin da na je ziyarar godiya ga ƙasashe mambobin ƙungiyar don gode musu saboda fahimtarsu da goyon bayansu, sannan kuma na tsunduma cikin shiga, irin wannan yarjejeniya, tare da kowane shugaban ƙasa da shugabannin ƙasashen yankin. Kungiyar Afirka, Afirka da Caribbean.
“Dukkanmu mun amince za mu yi aiki a cikinsa kuma muka samu Ministocinmu na tattalin arziki da na waje don samar da takardar aiki don tantancewa. Farfesa Bayo Adedeji da Dr. Arikpo daga Nijeriya da Mista Edem Kodjo da wani daga Togo da ma’aikatansu sun fara aiki, inda aka sa sauran ƙasashe mambobin su samar da takardar aiki don tantancewa.”
