Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Wasu ’yan bindiga sun kai hari da daddare a fadar wani basarake a ƙaramar Hukumar Kokona, inda suka yi ta harbe-harbe tare da yin awon gaba da sarkin.
A cewar wasu majiyoyi, Sangarin Dari, Emmanuel Omanji, an yi garkuwa da shi ne daga gidansa a daren ranar Larabar da ta gabata a lokacin da ‘yan bindigan suka kai samamen.
Masu garkuwa da mutanen sun shiga gidan ne ɗauke da manyan makamai inda suka yi ta harbe-harbe sannan suka yi awon gaba da basaraken zuwa wani wuri da ba a san inda suke ba.
Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan jihar Nasarawa (PPRO), Ramhan Nansel, ya tabbatar da sace basaraken.
Nansel ya ƙara da cewa, kwamishinan ’yan sanda a Nasarawa Shetima Jauro Mohammed, ya haɗa sashen yaƙi da masu garkuwa da mutane, sojoji, da ‘yan sintiri don gudanar da aikin ceto da nufin ceto wanda abin ya shafa tare da kamo waɗanda suka aikata laifin.
A cewarsa, kwamishinan ya nemi bayanai masu amfani da za su taimaka wajen yin aiki tare da rundunar ‘yan sandan Nijeriya.
Wannan dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mutane uku na Cocin Deeper Life Bible da ke yankin ƙaramar hukumar Akure ta jihar Ondo.
