

Daga MUHAMMAD AL’AMIN a Damaturu
A daidai lokacin da ya ke cika Shekaru shidda a karagar mulkin Jihar Yobe, Gwamna Mai Mala Buni, a ranar Alhamis ya gudanar da taron ji kai tsaye daga bakin al’ummar jihar, domin amsa tambayoyi da tsokacin jama’a dangane da ayyuka da manufofin gwamnatinsa.
Gwamnan ya ɗauki awanni yana amsa tambayoyi tare da tsokaci dangane da nasarorin da ya samu a cikin wannan tsakani, a fannonin harkokin ilimi, kiwon lafiya, abubuwan more rayuwa, tare da uwa uba, wato harkar tsaro.
Taron ya gudana a babban dakin taro na gidan gwamnatin jihar (Banquet Hall) dake Damaturu, wanda ya samu halartar Sarakuna, ƙungiyoyin matasa da mata, haɗi da ƙungiyoyin al’umma, da wakilan kafofin yaɗa labaru daban-daban da ke aiki a jihar.
Ofishin Mashawarci na musamman kan al’ammuran Rediyo, Talabijin, da Kafofin sadarwa na Zamani, Dakta Ibrahim Muhammad Yabani, ya nuna irin bajintar da Gwamna Buni ya nuna na tabbatar da samun haɗin kan al’ummar jihar.
Bugu da ƙari, Gwamna Buni ya bayyana jin-daɗinsa bisa ga irin cikakken goyon bayan da al’ummar jihar suke baiwa gwamnatinsa, inda ya danganta ci gaban jihar cewa ya gudana ne a tafarkin hadin kan al’umma, ya ce: “Wadannan shekaru shida sun gudana ne cikin karfafa gwiwa da hadin kai.”
“Tare da cikakken goyon bayan al’umma, mun shawo kan matsaloli da dama da jiharmu take fuskanta tare da samar da ci gaba mai dorewa.”
“Wasu daga cikin manyan nasarorin sun hada da ci gaban harkokin noma, habaka matasa, da samar da zaman lafiya mai dorewa, bayan rikicin Boko Haram.”
Taron ya bai wa ɗimbin mahalartansa damar yin tambayoyi inda Gwamna ya amsa, domin warware zare da abawa dangane da abubuwan da suka shigarwa jama’a duhu, daga cikin ayyukan da gwamnati take aiwatarwa tare da manufofin gwamnatinsa.
Mahalarta taron sun yaba wa gwamnatin jihar bisa ga ingantattun ayyukan more rayuwa da bunķasa jihar a fannonin rayuwa daban-daban.
Har’ilayau, Gwamna Buni ya buƙaci cigaba da samun goyon bayan al’umma, ya na mai jaddada haɗin-kai a matsayin tushen ci-gaba.
