
Daga BELLO A. BABAJI
Shahararren Attajiri kuma Shugaban Rukunin Kamfanin BUA, Alhaji AbdulSamad Rabi’u, ya bayyana gamsuwarsa ga yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da harkokin tattalin arziƙi da masana’antu a Nijeriya a yayin da gwamnatin ke cika shekaru biyu a mulki.
A cikin wata takarda da ya fitar mai taken ‘Shekara Biyu na Shugaba Tinubu: Duba da babin kasuwanci’, Abdulsamad ya bayyana cewa sauye-sauyen da Shugaba Tinubu ya aiwatar, musamman cire tallafin man fetur da haɗewar tsarin musayar kuɗaɗe (FX), na daga cikin muhimman matakan da suka ceto tattalin arziƙin ƙasar daga rugujewa.
A cewarsa, cire tallafin fetur da Shugaba Tinubu ya yi tun ranar farko da ya hau mulki, ya dakile barnar da ake yi wa tattalin arzikin Najeriya. Ya ce kafin cire tallafin, kasashe makwabta kamar Jamhuriyar Nijar da Benin na cin moriyar fetur din Najeriya wanda ake sayar da shi a kan kudi marasa yawa.
“A lokacin da na ziyarci Jamhuriyar Nijar, Shugaban kasar ya ce kaso 100% na fetur da suke amfani da shi daga Najeriya yake fitowa. Hakan yana nuna yadda tallafin man Najeriya ke amfanar da kasashen waje,” in ji shi.
Ya ƙara da cewa, cire tallafin ya rage shan man fetur da kashi 40 zuwa 50%, yana mai jaddada cewa yawan kudin da ake samu yanzu ana amfani da su wajen gina ababen more rayuwa da taimakawa jihohi.
Abdulsamad ya kuma bayyana cewa, kafin haɗewar tsarin musayar kuɗaɗe, yawancin ‘yan kasuwa sukan kwashe lokaci suna yawo a Babban Bankin Najeriya (CBN) domin samun dala a farashi na gwamnati. Amma yanzu, sabon tsarin shugaba Tibubu ya buɗe kuma yana aiki ba tare da matsin lamba ko neman alfarma ba.
“Na haɗu da Gwamnan CBN sau daya cikin shekaru biyu, sabanin da, inda sai ka kwana a Abuja domin samun dala. Yanzu muna samun dala daga kasuwa cikin sauki,” in ji shi.
Abdulsamad ya yaba wa gwamnatin Tinubu da kafa daidaito da bin doka cikin harkokin kasuwanci, inda ya bayar da misali da yadda aka rufe wani kamfanin su a Port Harcourt saboda son zuciyar wani babban jami’in gwamnati a baya, amma irin hakan bai sake faruwa da su yanzh ba.
“A yau, babu wanda zai iya tashi ya rufe kamfanin wani don kawai yana goyon bayan abokin gasar sa na kasuwa. Gwamnatin Tinubu ba za ta lamunci hakan ba,” in ji shi.
Alhaji Abdulsamad Rabiu ya ce, tun daga lokacin da Shugaba Tinubu ya hau mulki, kamfaninsu ya zuba sama da dala biliyan daya a Najeriya, musamman a bangaren abinci, makamashi da siminti. Ya ce karin kudaden shiga da gwamnati ke samu daga cire tallafin mai da hadewar kasuwar kudade, ya ba su damar tsara dogon zango na ci gaba.
Dangane da tsadar kayan abinci, Abdulsamad ya yaba wa Shugaba Tinubu bisa saukar da haraji kan shigo da shinkafa, wanda ya hana masu boye shinkafa samun sukunin kara farashi. Ya ce wannan mataki ya saukaka wahala kuma ya nuna hangen nesan Shugaba Tinubu.
A ƙarshe, Abdulsamad ya bayyana cewa, Najeriya na da komai da ake bukata: albarkatu, mutane da kwararru, kuma yanzu tana da shugabanci mai inganci. Ya bukaci ‘yan kasuwa da masu zuba jari su yarda da Najeriya kuma su ci gaba da zuba jari a cikinta.
“Abinda Shugaba Tinubu ya yi shi ne: ya cire tallafin fetur wanda shine mafi girman almundahana a tarihin tattalin arziƙinmu. Ya haɗe kasuwar kuɗaɗe. Ya dawo da daidaito da aminci a kasuwa. Wannan shi ne tubalin ci-gaban ƙasa,” inji shi.
