Sojoji sun kama ƴan Pakistan huɗu bisa hannu a munanan hare-hare a Arewa ta Gabas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Rundunar Sojojin Nijeriya ta kama ƴan ƙasar Pakistan guda huɗu kan zargin su da hannu a ayyukan ta’addanci a shiyyar Arewa masu Gabashin Nijeriya.

Kwamandan Atisayen ‘HAƊIN KAI’, Manjo Janar Abdulsalam Abubakar ya faɗi hakan a yayin ganawa da manema labarai na Hedikwatar Tsaro bayan ziyarar sansanin atisayen a Maidugurin Jihar Borno, ranar Laraba.

Ya ce, bincike ya nuna cewa ƴan ƙasar wajen da aka kama suna da hannu dumu-dumu a safarar makamai da horar da mayaƙan ƙungiyoyin ƴan ta’adda da ke ayyukansu a shiyyar.

Janar Abubakar ya bayyana cewa, bayyanar ƴan waje a matsalolin rashin tsaron Nijeriya ya taimaka wajen samun ƙarfin makamai ga ƙungiyoyin ƴan ta’adda kamar su ISWAP da JAS, lamarin da ya sa ake samun ƙaruwar hare-harensu a yankuna daban-daban na shiyyar.

Kwamandan ya yi kira da a kawo ɗauki a mataki na ƙasa-da-ƙasa domin kawo ƙarshen barazanar, yana mai cewa akwai buƙatar a faɗaɗa matakan sirri da haɗaka mai ƙarfi a tsakanin Nijeriya da ƙasashen maƙota domin daƙile ayyukan mayaƙan musamman waɗanda ke da alaƙa da iyakokin ƙasashen.

Babban jami’in ya ƙara da cewa, barazanar ƴan ta’addar tana harin Nijeriya ne a matsayinta na ƙasa ba iya jami’an tsaro ba, inda ya bada misali da rikicin Boko Haram da ISWAP waɗanda suna faruwa ne don nakasa Nijeriya.

Ya kuma yaba wa jajircewa da sadaukarwar jami’an sojoji wajen yaƙi a wurare mafiya haɗari a kowane lokaci kuma a kowane hali suka tsinci kansu, inda ya yi kira da a faɗaɗa hanyoyin ƙarfafa musu domin sauke nauyin da aka ɗora musu yadda ya dace, wanda ake fatan samun nasara matuƙar aka yi hakan.

By Babaji