
Daga BELLO A. BABAJI
Hukumar Shige da Fice (NIS) ta kama ƴan ƙasashen waje guda 127 a Unguwar Hotoro dake Ƙaramar Hukumar Nasarawa a Jihar Kano bisa zargin su da hannu a laifukan da suka shafi haramtattun ayyuka a yanar gizo da shige da fice ba bisa doka ba.
Hakan ya biyo bayan karɓar wasu ƴan Nijeriya guda 111 daga Niamey na ƙasar Jamhuriyar Nijar Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta yi a yunƙurinta na tallafa wa waɗanda suka dawo gida don raɗin kansu, kamar yadda hukumar ta wallafa ta kafar X.
Kwantirolan NIS na Jihar Kano, Kabir Ɗanja ya ce sun yi nasarar kamen ne a yayin wani atisaye, wanda aka gudanar a sakamakon samun sahihan bayanai na sirri game da wajen da suke gudanar da ayyukansu na damfarar ƴan Nijeriya.
Ya ce, an kama mutane 206 waɗanda daga ciki akwai ƴan Nijar guda 86, ƴan Chadi 41 da ƴan Nijeriya 80. Sannan guda 185 maza ne yayin da aka samu mata 21 acikin su, waɗanda dukkan su ƴan shekera 25 ne zuwa 35.
Bincike ya bayyana cewa, mafi yawancin ƴan wajen guda 127, sun shigo Nijeriya ne da haramtattun iyakoki, waɗanda kuma ba su da takardun shaidar zama da na tafiye-tafiye.
Kazalika, ya ƙara da cewa, an miƙa ƴan Nijeriyar guda 80 ga ƴan sanda.
Game da ƴan Nijeriya 111 da suka dawo gida daga Nijar, NEMA ta ce hakan ya samu ne bisa shirin Ƙungiyar Shige da Fice ta ƙasa-da-ƙasa (IOM) da haɗin-gwiwar hukumomin shige da fice.
Har’ilayau, hukumar ta ce mutanen sun haɗa da maza 87, yara maza takwas, mata guda takwas da kuma yara mata takwas.
