Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Ziyarar farko da Donald Trump ya kai gaɓar ta tsakiya da karyawa da Saudiyya ba ta yi wata fa’ida ta zahiri ga al’ummar Falasɗinawa da ke Gaza ba. Duk da ma wannan ita ce ziyarar Trump ta farko ƙetare a dawowar sa karaga karo na biyu amma hakan kamar kauda kai ne kan Gaza. An ga yarjeniyoyin kasuwanci na biliyoyin dala da Trump ya cimma nasara a Saudiyya, Katar da Daular Larabawa. Ni dai dama ban yi mamaki ba don na duba yadda siyasar duniya ta ke ne inda manyan ƙasashe masu ƙarfin makamai ke barazana ga sauran ƙasashe da zummar kare muradun su da yin sassauci ga wadanda su ka mika mu su wuya. Masu tunanin amfani da Larabci don tallafawa Larabawa a Gaza bai ma taso ba don shugabannin Larabawa na yin ta kan su ne ta hanyar neman dauwama kan mulki don haka ba za su iya sadaukar da mulkin su don samawa Falasɗinawa maslaha ba. Hakana masu cewa addinin Musulunci ya haɗa Falasɗinawa da Larabawa don haka a kai mu su ɗauki ba daidai ba ne don Falasɗinawa na da Musulmi da mabiya addinin Kirista kuma su na aiki tare don kwatawa ƙasara su ‘yanci. Mun san in ma addinin ne Saudiyya ce kan gaba wajen ba da gudunmawar kuɗi da ba da guraban karatu ga ɗalibai daga ƙasashe masu ƙaramin ƙarfi. Baya ga waɗannan hanyoyin ba zai yiwu Saudiyya ta iya fitowa ƙarara ta yi cara ta marawa Gazawa baya ba amma duk da haka za ta iya yin Allah wadai in an jefawa boma-bomai kan yankunan Gaza. Hada kai da Amurka na da muhimmanci ga Saudiyya, ƙatar da Daular Larabawa don duk ƙasashen uku na ƙarƙashin mulkin mulukiyya ne da su ke ɗaukar matakan gayawa jini na wuce ga duk yunƙurin kawo batun dimokraɗiyya ko juyin juya hali da wasu ke fatar gani. Duk hakan ba zai yi nasara ba sai sun kyautatawa ƙasashen yamma musamman Amurka baya don kar ta fantsama mu su fitina da za ta kawo ƙarshen daular su. Kazalika in ma wani ko wata ƙungiya ta na neman daga yatsa ga tsarin mulukiyya na ƙasashen sai Amurka ta kau da kai don ɗanyen ganyen da ta ke yi da ƙasashen. Ai na sha kawo misalign kisan gilla da aka yi wa ɗan jaridar nan na Saudiyya Jamal Kashoggi a Istanbul ɗin Turkiyya kuma a ka gabatar da hujjoji na nuna lallai Saudiyya ta turo ‘yan aiki da cikawa su ka kashe Kashoggi da daddatsa naman sa da salwantar da gawar sa. Amurka ƙarƙashin Trump a lokacin ta kau da kai da nuna tamkar lamari ne na cikin gidan Saudiyya. Kar ma mu damu don ɗorewar mulkin mulukiyya sai da irin hakan don sabon zamani ba zai cigaba da tafiya da irin waɗannan gwamnatocin ba don haka da zarar sun ji karas sai su kararas! Duk wanda ya nuna mu su yatsa za su fille ta. Mai yi mu su addu’a ma yaya ya kare balle mai suka. Kawai zaluncin da a ke yi wa Falasɗinawa a Gaza ba zai ɗore har abada ba. Da yawa sun rasa ran su a gwagwarmyar neman ‘yancin ƙasar su ta haihuwa kuma wannan mutuwa da su ke yi ba ta sa wasu na baya firgita da daina yunƙuri ba. Zafi da gudun murƙushewa ya sa gwamnatin Falasɗinawa ta birnin Ramallah ƙarƙashin Mahmud Abbas yin kadaran-kadahan don gudun fuskantar kisa ko turewa daga karaga. Ya zama wajibi Falasɗinawa kakaf su ƙara haɗa kai don hakan ne zai ba su nasara duk jinin kuwa da a ka kwararar mu su.
HARIN ISRA’ILA A GAZA YA YI SANADIYYAR MUTUWAR FALASɗINAWA 82:
Mummunan harin da Isra’ila ta kai Gaza a Laraba ya yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 82 ciki kuwa har da jinjiri mai kwana 7.
Isra’ila na cigaba da kai hare-hare duk da yadda wasu ƙasashen duniya ke tir da matakin da kan zama sanadiyyar mutuwar mata da ƙananan yara.
Duk da Isra’ila ta bar motocin kayan agaji su shiga Gaza amma ta tare motocin daga isa inda ya dace na can cikin yankin na Gaza.
Jami’an agaji na jiran samun kayan don rabawa masu matuƙar buƙatar tallafin amma sai Isra’ila ta tilasta sauke kayan da loda su a wasu sabbin motoci.
Wasu ‘yan rajin kare muradun Yahudawa sun nuna ɓacin ran su ga barin kayan agajin su shiga Gaza alhali akwai sauran kamammun Isra’ilawa a hannun Hamas.
Kazalika wasu jami’an diflomasiyya ma sun auna arziki yayin da su ka ziyarci yankin Jenin da ke yammacin kogin Jodan inda Isra’ila ta mamaye.
Jami’an da su ka haɗa da wakilai daga Turai na zantawa da manema labaru a mashigar wani sansanin ‘yan gudun hijira yayin da su ka ji ƙarar albarusai da hakan ya sa su ka bar wajen don gujewa ran su.
Har yanzu Isra’ila ba ta komai a kan hakan ba.
Isra’ila ta ce za ta amince da dakatar da dirar miƙiya da ta ke yi wa Gaza idan an saki duk kamammun da ke hannun Hamas da kuma murƙushe Hamas ɗin ko kuma tura su gudun hijira.
A na ta ɓangare Hamas ta ce ba za ta yarda da sako sauran kamammun kimanin 24 ba sai Isra’ila ta tabbatar dakatar da yaƙin da janyewa rankatakab daga Gaza.
Daidai lokacin da hare-haren ke ƙara zafi wani mutum ya buɗe wuta kan ma’aika biyu na ofishin jakadancin Isra’ila a Amurka da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar su.
Mutanen biyu mace da namiji na fitowa ne daga gidan tarihi na Yahudawa a Washington yayin da mai riƙe da bindigar mai suna Elias Rodriguez ya buɗe mu su wuta.
Bayan buɗe wutar Rodriguez daga Chicago ya shiga gidan kayan tarihin ya na mai cewa a ba wa Falasɗinawa ‘yancin su inda ya ba da kan sa a ka kama shi.
Isra’ila ta ce mutanen biyu da ke shirin ɗaura alƙawarin aure a birnin Kudus sun haɗa da ma’aikaciyar ofishin jakadancin Ba’amurkiya inda namijin kuma Bayahude ne.
Nan take Firaministan Isra’ila Benjmain Netanyahu ke nuna ɓacin ran ga harin da nuna Isra’ila na fama da nuna ma ta kiyaiya ko zuga mutane su yi ma ta bore.
A wani ɓangaren da alamu Afurka ta kudu da ta shigar da Isra’ila kara a kotun duniya don a tuhume tad a kisan ƙare dangi kan Gazawa na fuskantar wariya daga shugaba Trump. Amurka ce dama kan gaba wajen marawa Isra’ila baya da hawa kujerar na ki a kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin Duniya a duk lokacin da za a iya ɗaukar matakin ba sani ba sabo kan Isra’ila.
Shugaban Afurka ta kudu Cyril Ramaphosa ya dage don fahimtar da shugaban Amurka Donald Trump cewa ba gaskiya ba ne labarin yin kisan ƙare dangi ga Turawa manoma.
Trump dai ya yayata cewa a na kisan ƙare dangi kan manoma fararen fata a Afirka ta Kudu da ma kwace mu su filayen noma.
Wannan matsaya ta sa har Trump ya yi alwashin bada mafakar siyasa ga Turawan Afurka ta kudu a Amurka.
A ganawa da fadar White House Ramaphosa ya ce sam labarin ba gaskiya ba ne kuma ɗaya ma daga faya-fayan da Trump ya nuna na hakan ne shaida bayanai ne daga ‘yan adawa da ba ra’ayin gwamnatin Afurka ta kudu ba ne.
Cyril Ramaphosa ya ce ya na ganin sai Trump ya ji bayanai daga al’ummar Afirka ta Kudu kafin ya sauya ra’ayin sa.
Kazalika Ramaphosa ya ce akasarin ma waɗanda su ka fi shan wuya a fitinar baƙaƙen fata ne.
Babban mai ba wa Trump shawara Elon Musk wanda ɗan asalin Afurka ta kudu ne na nan a wajen ganawar.
Masu sharhi da ke tausayawa Falasɗina na nuna marawa Falasɗinawa da Afurka ta kudu ke yi ne ya jawo ma ta karantsana daga Amurka. ƙasar ma ta samu sassauci ne don ta na mulki ne da ba shi da alaƙa da wani addini kuma mutanen ƙasar sun yi suna a duniya lokacin da su ka yaƙi mulkin wariyar jinsi ko launin fata daga Turawa. Hatta Jamus ma ta yi matuƙar jin haushin Afurka ta kudu don tsayin daka a kotun duniya da zummar ɗaukar mataki kan Isra’ila. Irin wannan goyon baya da Isra’ila ke samu daga ƙasashen yamma ya sa ta na ware kafa da yin gaban kan ta wajen hare-hare kan makwabta. Ai mun san cewa matakan ko hukuncin kotun duniya bai yi tasiri kan Isra’ila. Ban da ma rashin tasirin har ya kai ga Isra’ila shashantar da batun da caccakar kotun duniyar lamarin ya sha ruwa.
KAMMALAWA
Da dai mutuwa ko kisa zai kasha gwagwarmayar Falasɗinawa da tuni an daina jin labarin su ko sun zama bayi a hannun Yahudawa. Kazalika ko Larabawa sun mara mu su baya ko sun ki mara mu su baya ba zai sa Isra’ila ta yi barci da ido biyu rufe duk da mallakar makaman ƙare dangi. ɗaiɗaikun mutane da ke marawa Falasɗinawa baya su cigaba da tayawa da addu’a don da alamu ko kuɗi a ka tara gudunmawa zai yi wuya su isa hannun waɗanda a ka yi abun damun su don tsaurara hanyoyin da Isra’ila ta yi. Allah ba ya barci.
