Conference League: Chelsea ta murƙushe Real Betis a wasan ƙarshe

Spread the love

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta lashe kofin UEFA Conference League bayan doke Real Betis da ci 4-1 a wasan ƙarshe da aka buga ranar Laraba. Wannan shine karo na farko da ƙungiyar ta samu kofi a ƙarƙashin sabon kocinta Enzo Maresca.

Real Betis ce ta fara jefa ƙwallo a ragar Chelsea a minti na 9 ta hannun dan wasan Morocco, Abde Ezzalzouli, bayan wani kyakkyawar bugun baya daga Isco. Sai dai bayan hutun rabin lokaci, Chelsea ta dawo da ƙarfi inda Enzo Fernandez, Nicolas Jackson, Jadon Sancho, da Moises Caicedo suka zura ƙwallaye huɗu.

Wannan nasara ta kawo ƙarshen shekaru huɗu da Chelsea ba ta lashe wata gasa ba tun bayan nasarar Champions League a 2021, kuma ta cika jerin kofunan Turai da ƙungiyar ta taɓa lashewa a tarihi.

By ukarofi