*Cacekuce ya ɓalle tsakanin Fadar Shugaban ƙasa da ‘yaran’ Buhari
*Ba Tinubu ne ya sa Buhari ya ci zaɓe a 2015 ba – Boss Mustapha
*Tinubu ne ya buɗe wa Buhari ƙofa — Fadar Shugaban ƙasa
*Ba zan juya wa APC baya ba, inji Buhari
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Daga dukkan alamu musayar yawu da cecekucen siyasa ya ɓalle a tsakanin Fadar Shugaban ƙasa da wasu daga cikin manyan magoya bayan tsohon Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari kan rawar da Shugaban ƙsaa mai ci, Bola Ahmed Tinubu, ya taka a zaɓen 2015, wanda ya kai Buhari ga samun nasarar lashe shi a karon farko bayan ya gwada sa’arsa a baya sau uku ba tare da ya kai gaci ba.
Idan za a iya tunawa, rusasshiyar Jam’iyyar ACP, wacce Tinubu ke jagoranta, na daga cikin jam’iyyun haɗakar da suka kafa APC suka yi gangami suka kayar da PDP mai mulki a wancan lokacin. Sai dai kuma a zaɓen 2023, wanda shi Tinubun ya tsaya takara, ana ganin cewa, bai samu cikakken goyon bayan Gwamnatin Buhari ba, duk da cewa, a ƙarshe dai shi ya samu nasarar lashe zaɓen.
Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya ce ba Shugaban ƙasa Bola Tinubu kaɗai ne ya sa Muhammadu Buhari ya ci zaɓensa a shekarar 2015 ba.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a Abuja ranar Laraba, yayin ƙaddamar da littafin da mai magana da yawun tsohon Shugaba Buhari, Malam Garba Shehu ya wallafa kan abubuwan da ya gani a zamanin mulkinsu.
Buhari dai ya shugabanci Nijeriya ne daga shekarar 2015 zuwa 2023.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci ƙaddamar da littafin akwai tsohon Shugaban ƙasa na mulkin soja, Yakubu Gowon da tsohon Mataimakan Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya mai ci, George Akume da dai sauransu.
Idan za a iya tunawa, yayin wani taron neman goyon bayan wakilan jam’iyyar APC a jihar Ogun a a ranar ɗaya ga watan Yunin 2022 gabanin zaɓen fi-da-gwani na jam’iyyar, Tinubu ya yi iƙirarin cewa da ba don shi ba, da Buhari bai ci zaɓen 2015 ba.
To sai dai da yake gabatar da muƙala a kan nasarorin mulkin Buhari, Boss ya ce akwai jiga-jigan APC da dama da suka taimaka aka samu nasarar, ba wai Tinubu shi kaɗai ba, yana mai cewa gaskiya da riƙon amanar Buharin ma sun taka rawa.
Ya ce, “Akwai kuma ɓangarorin jam’iyyar CPC ita kanta, akwai na ANPP da na ACN da APGA da kuma wani tsagi na PDP da ya ɓalle ya shigo cikin haɗakar APC. Tinubu ya taka rawar gani, sannan Sanata Ali Modu Sheriff wanda tsohon Shugaban Kwamitin Amintattu ne na ANPP shi ma ya yi ƙoƙari.
“Haɗakar ta yi nasarar kafa tarihin farko a Nijeriya inda aka kayar da shugaba mai ci, kuma gaskiya da riƙon amanar shi su ne a kan gaba wajen samun wannan nasarar.
“A ɓangarenmu na ACN, ba na so na tayar da ƙura, amma maƙasudin haɗa majar ita ce don a tsayar da Buhari takara saboda mun kalli alƙaluman ƙuri’unsa na baya.
“A shekara ta 2003, an fafata tsakanin Buhari da Obasanjo, inda Buharin ya samu ƙuri’a miliyan 2.7. A 2007 kuma, ya samu miliyan 6.6, sai a 2011 kuma ta ƙaru zuwa 12.2.
“Lokacin da muka yi ƙoƙarin haɗa APC, jam’iyyar CPC ta Buhari na da Gwamna ɗaya, ACN na da shida, sai ANPP na da uku. Idan ka haɗa jimlar ƙuri’un da muka samu a zaɓen Shugaban ƙasa a 2015 kuma miliyan 15.4 ne.
“Ka ga ke nan ƙuri’un da muka ƙara wa Buhari bayan kafa APC a kan ƙuri’u miliyan 12.5 ɗin da Buhari ya zo da su daga CPC su ne miliyan uku,” inji Boss Mustapha.
Sai dai hadimin Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, kan Harkokin Yaɗa Labarai, Temitope Ajayi, ya mayar wa tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha martani kan kalaman nasa.
Ajayi, ya ce Buhari yana da ƙarfi sosai a Arewa amma hakan bai hana shi faɗuwa zaɓukan 2003, 2007 da 2011 ba.
Ya bayyana cewa a zaɓen fidda gwanin jam’iyyar APC da aka yi a 2014, Tinubu ne, ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin Buhari ya lashe.
Ya ce Tinubu ne ya shawo kan gwamnonin APC da wakilan Kudu maso Yamma su mara wa Buhari baya a lokacin zaɓen da aka yi a filin wasa na Teslim Balogun a Legas.
Ya ce ba don wannan goyon baya ba, da Buhari bai samu tikitin takarar shugaban ƙasa ba.
Ajayi, ya ce bai dace a raina ƙoƙarin Tinubu da sauran waɗanda suka taimaka wa Buhari ba.
Ya ce Boss Mustapha bai faɗi gaskiyar abin da ya faru ba.
“Mu bar maganar babban zaɓen da Buhari ya lashe. Ai da bai zama ɗan takara a jam’iyyar APC ba, da ba zai taɓa zama shugaban ƙasa ba.
“Kuma da babu goyon bayan Tinubu a zaɓen fidda gwanin APC da aka yi a Legas a 2014, da Buhari bai lashe ba.”
Shi kuwa, tsohon Shugaban ƙasa Buhari ya jaddada biyayyarsa ga Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) tare da yin watsi da raɗe-raɗin rashin jituwa da Shugaba Bola Tinubu.
Da yake magana a cikin shirin mintuna 30 na Trust Tɓ a ranar Talata, mai magana da yawun Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce babu wata rashin jituwa a tsakanin shugabannin biyu ko tsakanin gwamnatocin su.
Da yake ambaton Buhari, Shehu ya ce, “Ba zan taɓa yin butulci ba, ba zan taɓa cin amanar jam’iyyar da ta ba ni damar yin wa’adi biyu ba.” Ya jaddada cewa Buhari ya ci gaba da godiya ga jam’iyyar APC da ta samar da tsarin da ya kai ga zaɓen sa bayan wasu yunƙuri har sau uku da bai kai ga nasara ba.
“APC ta ba shi damar yin wa’adi biyu, wanda ya ci gaba da godiya,” inji Shehu.
Da yake magana kan rahotannin dambarwar siyasa a cikin jam’iyya mai mulki, Shehu ya ce irin waɗannan iƙpirari na hasashe ne kuma baya nuna wani matsayi ko matsayi na Buhari.
Da yake tsokaci kan asalin jam’iyyar, Shehu ya tuno da gagarumin ƙalubalen da aka fuskanta wajen kafa jam’iyyar APC a shekarar 2014. Ya kuma bayyana cewa waɗanda suka gane wa idanunsu yadda lamarin zai yi wuya su durkusar da jam’iyyar a yanzu.
“An ɗauki gagarumin aiki, kuzari, da sadaukarwa don an kafa APC, domin ‘yan adawa masu tsananin son haduwa su haɗu,” inji shi.
“Sun gwada ɗaya, biyu, sau uku, kuma sun kasa, amma a wannan lokacin, sun haɗu a shekarar 2014, suka kafa jam’iyya, suka tsaya takara, sun yi nasara.”
A cewar Shehu, Buhari na ci gaba da haɗa kai da jam’iyyar APC kuma ya ci gaba da jajircewa wajen ganin an samu haɗin kai da kwanciyar hankali a jam’iyyar.
