Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
An tsige Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, sanata mai wakiltar Kogi ta tsakiya a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa mai kula da ‘yan ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ne ya bayyana hakan a zaman majalisar na ranar Alhamis.
Daga nan ne shugaban majalisar dattawan ya bayyana Sanata Aniekan Bassey na jihar Kuros Riba a matsayin wanda zai maye gurbin ta.
Tun da farko an naɗa Sanata Akpoti-Uduaghan a matsayin shugabar kwamitin majalisar dattawa kan abubuwan cikin gida bayan rantsar da ita a matsayin Sanata a watan Nuwamba 2023.
Sai dai kuma a ranar 4 ga watan Fabrairun 2025, Shugaban Majalisar Dattawa Akpabio ya jagoranci yin garambawul na shugabancin kwamitoci, inda ya cire ta daga wannan kwamiti ya naɗa ta shugabar kwamitin ‘yan aasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu.
Naɗin aka yi mata a watan Fabrairu ya haifar da cece-kuce domin lamarin ya faru ne jim kaɗan bayan da Sanata Akpoti-Uduaghan ya sa ido sosai kan hukumomin mai da iskar gas.
Wasu masu lura da al’amuran yau da kullum dai sun yi nuni da cewa wata ƙila dalilai na siyasa ne ya sa aka tsige ta.
Zamanta a matsayin shugabar kwamatin ‘yan ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu ya sake samun cikas, a ranar 6 ga Maris, 2025, an dakatar da ita na tsawon watanni shida bisa zargin rashin ɗa’a. Ko da yake dakatarwar ta dakatar da ayyukan kwamitinta na wani ɗan lokaci, ta ci gaba da zama shugabar kwamitin har zuwa ranar Alhamis.
Yayin da Sanata Bassey a yanzu ke riƙe da shugabancin kwamitin ‘yan ƙasashen waje da ƙungiyoyi masu zaman kansu, majalisar dattawa ta rufe babin jagorancin Akpoti-Uduaghan na ƙanƙanin lokaci na kwamitocin dabaru guda biyu.
