Yadda aka riƙa farautar Bello Adoke a duniya kan batun yarjejeniyar OPL 245 – Jonathan

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan ya bayyana tsohon Atoni Janar na ƙasa (AGF) kuma Ministan Shari’a, Mohammed Bello Adoke, a matsayin mutumin da aka riƙa farautar sa a duk faɗin duniya sakamakon taƙaddamar yarjejeniyar OPL 245.

Jonathan ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Alhamis a wurin taron tunawa da Adoke mai taken “OPL 245: Asalin labarin dala biliyan 1.3 na man fetur ɗin Nijeriya.” Littafin ya ba da bayanan sirri na Adoke game da shari’a, siyasa da ma’amala mai rikitarwa wanda ya mamaye kanun labarai sama da shekaru goma.

Da yake gabatar da jawabinsa ta bakin wani wakili, tsohon shugaban majalisar dattawa, Pius Anyim, Jonathan ya koka da yadda lamarin ya zama cin zarafi ga wasu manyan jami’an gwamnatinsa a siyasance jim kaɗan bayan ya bar mulki a shekarar 2015.

“Mawallafin wannan tarihin, Bello Adoke, shi ne babban lauyan gwamnatin tarayya a wancan lokacin. An farauto shi a faɗin duniya,” inji Jonathan.

“Amma a yau yana raye, yana cikin ƙoshin lafiya, kuma ya zo ne domin ya ba da labarinsa, don haka bari in yi amfani da wannan damar don taya  Bello Adoke, abokina da kuma ɗan uwana murna, bisa bajintar da ya yi, kuma in ce na ji daɗin kasancewa tare da kai wajen murnar wannan nasara.”

Tsohon shugaban ƙasar ya ce, labarin OPL 245 da aka fi sani da ɗaya daga cikin rigingimun da suka shafi shari’a a Nijeriya, siyasa ce da kuma makami da gwamnatin da ta gaje shi, wanda a cewarsa, ya fara abin da mutane da yawa suka ɗauka a matsayin farautar wasu manyan jami’an gwamnatinsa.

Jonathan ya yaba da matakin da Adoke ya ɗauka na buga littafin, inda ya bayyana hakan a matsayin jajircewa kuma aikin da ya dace don kare gaskiya da kuma ba da gudunmawa ga al’amuran ƙasa na Nijeriya kan adalci da mulki.

Asalin ƙoƙarin marubucin na rubuta tarihin nasa ba wai kawai don a daidaita al’amura ba ne amma don bayar da gudunmawa wajen tabbatar da gaskiya da adalci a matsayin babban ginshiƙan gina ƙasa,” inji shi.

A yayin taron, Adoke ya bayyana cewa ya yafe wa duk wanda ya taka rawa wajen matsalolin da suka biyo bayan shari’ar OPL245 da suka shafe shi. 

Adoke ya ce, ba cin mutuncin wasu ba ne manufarsa wajen wallafa littafin, illa bayyana gaskiya da kare sunansa da kuma fayyace abubuwan da suka faru a yarjejeniya da ta shafi arzikin ƙasa.

Ya ce, “Na rubuta wannan littafi ne domin fayyace tarihi, ba domin in ci zarafin wani ba. 

“A yarjejeniyar OPL245 da aka kammala a 2011, na taka rawa a lokacin ne domin kare muradun tattalin arzikin ƙasa, ko da yake ban kasance cikin waɗanda suka fara yarjejeniyar tun a 2006 ba.”

Adoke ya zargi hukumar EFCC da ɓoye hujjoji da tsoratar da shaidu domin cimma nasarar gurfanar da shi a gaban kotu.

Ya ce abin takaici ne yadda wasu suka ɗauki nauyin ɓata masa suna, har ya rasa mutunci da zaman lafiyar iyalinsa.

By ukarofi