Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya buƙaci ’yan Nijeriya da su daina saka musu ido da tunanin cewa sanatoci suna cikin majalisar dokokin ƙasar ne domin wawusar kuɗi, inda ya ce da yawa daga cikin tsofaffin ‘yan majalisar na fama da rashin kuɗi bayan sun bar mulki.
Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa kan sabuwar dokar gyaran wutar lantarki wadda ke neman warware matsaloli a ɓangaren samar da lantarki.
A cikin jawabinsa, Akpabio ya bayyana cewa babu yadda za a samu ci gaban masana’antu a ƙasar nan idan babu wutar lantarki. Ya ce kowa na fatan a yi garambawul gaba ɗaya ga bangaren wutar lantarki.
Akpabio ya ce gyaran dokar zai taimaka wajen sauya tsarin wutar lantarki gaba daya domin samar da ci gaba ga masana’antu da aasa baki ɗaya.
A cewarsa, jama’a na ganin ‘yan majalisa na neman kuɗi ne kawai, amma a gaskiya suna sadaukarwa ne domin cigaban ‘ya’yansu da al’umma gaba ɗaya.
Akpabio ya ce, “Mutane na tunanin muna nan a Majalisar Dattawa don neman kuɗi, ba tare da sanin cewa muna nan ne domin sadaukarwa ga al’ummomin gaba ba.”
Sabon ƙudirin na majalisa zai taimaka wajen kaucewa rikice-rikice na doka tsakanin gwamnati da jihohi game da harkar wutar lantarki.
Za a kuma ƙarfafa batun ɗaukar nauyin bangaren wutar lantarki tare da samar da tsari mai inganci na hulɗa da al’umma da ma’aikata.
Sanata Enyinnaya Abaribe, wanda ya ɗauki nauyin ƙudirin, ya ce ana so a cire ruɗani daga dokar da aka yi a baya domin ta fi sauƙi da fahimta.
Za a kara ƙarfi wajen hukunta masu lalata kayan aikin wutar lantarki da samar da kariya ga al’ummomin da masu wutar ke aiki a cikinsu.
Majalisar ta tura ƙudirin zuwa kwamitin wutar lantarki domin ci gaba da nazari, inda ake sa ran rahoto zai dawo a cikin makonni shida.
