Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
’Yan Nijeriya da dama sun nuna matuƙar damuwa dangane da amincewar cibiyar horar ta ‘BokoHaram Training Hub’ da ‘Nigeria Must Scatter’, da sauran su a matsayin sunayen kasuwanci da sabuwar tashar rajista ta Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci (CAC) ta amince da su, inda suka zarge ta da ba da fifiko ga tsarin amincewa da sauri ta na’ura mai sarrafa kanta maimakon bin hanya mai inganci da tsaro.
A ranar 1 ga Yuli, 2025, CAC ta ƙaddamar da wata sabuwar hanyar rajistar mai amfani da bayanan sirri mai suna Intelligent Company Registration Portal (ICRP) 3.0 wanda ya yi alƙawarin haɗa kasuwanci cikin mintuna 30.
A cewar hukumar, an ɗauki wannan matakin ne domin a samu sauƙin gudanar da harkokin kasuwanci a Nijeriya, musamman ma masu ƙanana da matsakaitan sana’o’i.
Majiyoyi sun bayyana cewa kwanan nan tsarin ya amince da yin rajistar sunayen kasuwanci kamar “Cibiyar Kai Wa ’Yan Bindiga Abinci”, “Cibiyar Horar da Boko Haram”, “Kamfanonin ƙera Abubuwan Fashe”, da Kamfanonin Watsewar Nijeriya – wanda a da ƙwararrun jami’an CAC za su yi watsi da su nan take.
Wannan lamari ya haifar da damuwa mai tsanani game da haɗarin rashin sa ido a cikin muhimman ayyukan gwamnati.
