Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Makarantun Gaba da Sakandire ta ƙasa (NECO) ta sanar da fitar da sakamakon Jarrabawar Kammala Karatu (BECE) na shekarar 2025.
An bayyana hakan ne a wata sanarwa da muƙaddashin daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na NECO, Azeez Sani ya fitar ranar Laraba.
ɗalibai 179,201 ne suka yi rijistar jarrabawar a darussa 12, kamar yadda muƙaddashin daraktan hulza da jama’a na hukumar Azeez Sani ya bayyana.
Jarrabawar wacce ta fara a ranar 12 ga Mayu, 2025, an kammala ta ne a ranar 23 ga Mayu, 2025.
Azeez ya bayyana cewa an fitar da sakamakon jarrabawar ne biyo bayan nasarar kammala taron kwamitin bada lambar yabo ta BECE na shekarar 2025 da aka gudanar a hedikwatar hukumar da ke Minna.
A yayin taron, shugabar kwamitin bayar da lambar yabo, Dakta Folake Olatunji Daɓid, Darakta a fannin ilmin asali na ma’aikatar ilimi ta tarayya, ta bayyana gamsuwarta da yadda ake samun nasarar fitar da sakamakon.
“Taron kwamitin karramawar ya kuma samu halartar wasu shugabannin makarantun Sakandare na ƙasar nan da kuma hukumar kula da NECO.
A halin yanzu, Kwamitin Kyautar ya amince da Kwanan wata da Jadawalin 2025 na BECE.
Sanarwar ta ƙara da cewa, “An shirya gudanar da jarrabawar ne a ranakun 23 da 24 ga watan Yuli, 2025 don nazarin Lissafi da Ingilishi.”
