Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Tun a ranar da wasu manyan adawa a Nijeriya suka bayyana samar da haɗaka a Jam’iyyar ADC aka fara mayar da yawu tsakanin ɓangarorin masu ruwa da tsaki a siyasar Nijeriya, musamman jam’iyyun adawa, inda yanayin ke nuni da cewa, ba lallai ne komai ya tafi salim alim, kamar yadda aka yi zato tun farko ba.
Wannan ya sanya Blueprint Manhaja ta tattaro akasarin bayanai na abubuwan da suke faruwa daga ayyana haɗakar zuwa haɗa wannan rahoto.
Dalilinmu na zaɓar ADC a matsayin jam’iyyar haɗaka, inji su:
A ranar Laraba ne manyan ’yan adawar siyasa na Nijeriya suka tabbatar da amincewa da jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) a matsayin wadda za su yi aiki da ita domin tunkarar zaɓen 2027.
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, wanda jigo ne a haɗakar ya ce: “mun kwashe wata tara zuwa shekara ɗaya muna tattaunawa domin ganin yadda za mu haɗa kanmu mu shiga jam’iyya ɗaya da ba za a iya soke rajistarta ba, mu gyara jam’iyyar da shugabancinta da aƙidarta da fito da tsarin da zai ceci ƙasarmu daga wannan hali da aka shiga.”
Hakan na zuwa ne bayan yunƙuri daban-daban da ‘yan adawar suka yi na ganin sun samar da ƙwaƙƙwarar adawa da za su iya tunkarar shugaban ƙasar mai ci Bola Ahmed Tinubu, wanda suke zargi da gazawa a mulkinsa.
Ana iya cewa wannan mataki ya kawo ƙarshen raɗe-raɗi da hasashen da ake yi na hanyar da ‘yan adawar za su bi domin tunkarar babban zaɓen na 2027 na Nijeriya.
A baya ‘yan adawar sun yi yunƙurin ganin an yi wa sabuwar ƙungiyar da suka fito da ita (ADA) rajista domin amfani da ita a matsayin lemar ‘yan adawa.
Sai dai har yanzu hukumar zaɓe ta ƙasar INEC ba ta kammala dubawa ba balle ta sanar da amincewa ko rashin amincewa da bukatar ta ‘yan adawa.
Da dama daga cikinsu sun zargi INEC ɗin da yunƙurin daƙile ƙoƙarinsu na kafa sabuwar jam’iyyar, lamarin da hukumar ta musanta.
Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya ce hakan ne ya sanya suka yanke shawarar neman jam’iyyar da ke da rajista a ƙasa domin ɗora tafiyarsu a kai.
“Mun yanke shawarar neman jam’iyya da ba ta da matsala mu shiga, amma ban da haka za mu ci gaba da ƙoƙarin rajistar sabuwar jam’iyyarmu, ko da gwamnati za ta yi ƙoƙarin ta shiga (ADC) ta kawo mana matsala.
“Wannan shigar mu ADC na wucin-gadi ne kuma idan aka samu jam’iyyar da ba ta da matsala” a cewar El-Rufa’i za su koma cikinta.
Sai dai Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa har yanzu bai bar SDP ba – wadda a yanzu ya yi zargin cewa “wasu shugabannin jam’iyyar sun riga sun zama ma’aikatan gwamnati…suna son su ɓata maganar SDP ta zama jam’iyyar haɗaka”.
ɗaya daga cikin manyan zarge-zargen da ‘yan adawar ke yi wa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da jam’iyyar APC mai mulki shi ne haifar da ruɗani a cikin jam’iyyun adawa, duk kuwa da cewa shugaban ƙasar ya musanta hakan.
Ko a cikin bayanin da El-Rufa’i ya yi wa manema labarai bayan taron na ranar Laraba, ya ce “gwamnati ta lalata jam’iyyar PDP, ta kawo rudani a jam’iyyar LP da kuma NNPP.”
Sai dai ya ce a wannan karo ‘yan adawar sun yi shirin yadda za su kauce wa hakan a jam’iyyar ADC.
“A nan gaba ƙila mu canza wa jam’iyyar nan (ADC) suna, kila ma mu canza mata fasali, in kuma gwamnati ta ɓata ta dukkan mu za mu koma wata jam’iyyar guda ɗaya tak, da mabiyanmu da ‘yan takarar,u domin a fuskanci wannan gwamnatin,” inji El-Rufa’i.
A ranar bikin zagayowar dimokuradiyyar Nijeriya da ya gabata dai, shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya kore yiwuwar mayar da Nijeriya mai bin tsarin jam’iyya ɗaya, kamar yadda ‘yan adawa ke zargi.
Sai dai ya ce “ina jin daɗin ganin ku (‘yan adawa) a tagayyare” tare da cewa ba zai taimaka musu su ɗinke ɓarakar da suke fuskanta ba.
Babbar jam’iyyar adawa ta Nijeriya PDP na fama da matsaloli na cikin gida, lamarin da ya kai har gaban kotu.
Sai dai a cikin makon na ta gudanar da taro inda ta bayyana cewa ta ɗunke dukkanin ɓarakar da take fama da ita.
Haka nan jam’iyyun LP da NNPP duk suna fama da matsalar rikici na cikin gida.
A baya-bayan nan jam’iyyar SDP da ta fara samun tagomashi bayan komawar tsohon gwamnan na jihar Kaduna, ita ma ta shiga jerin jam’iyyun adawa masu fama da rikici.
Wasu daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar na zargin shugabanta da wandaƙa da kuɗi, sai dai a cikin wata tattaunawa da BBC, Shehu Musa Gabam ya musanta zarge-zargen.
Atiku Abubakar ne ya zo na biyu a yawan ƙuri’u a zaɓen shugaban Nijeriya na 2023 a bayan Shugaban ƙasa Bola Tinubu.
Wata babbar ayar tambaya da ake ɗora wa haɗakar ‘yan adawar ita ce yadda ake kallon cewa ta haɗa mutane daga jam’iyyu daban-daban masu buri ɗaya – wato shugabancin Nijeriya.
Wani abu da masu lura da harkar siyasa a ƙasar ke ganin cewa idan ba a yi sa’a ba, ko ba jima ko ba daɗe za a iya samun ɓaraka a lokacin da aka zo batun fitar da ɗan takara.
Yanzu haka mutane biyu da ake wa kallon ƙashin bayan haɗakar – Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP da kuma Peter Obi na LP duk sun yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen da ya gabata, kuma ana ganin cewa yanzu haka ma take-taken kowannensu na nuna cewa suna son sake tsayawa takara.
Sai dai Nasir El-Rufa’i ya ce jigon hadakar tasu shi ne ajiye buri domin samar da nagartacciyar jam’iyya.
“Tun da muka fara zazzagayawa mun ce musu ku ajiye burinku mu zo mu yi jam’iyya ƙaƙƙarfa domin hada kai a kori wannan jam’iyyar da wannan gwamnati,” in ji El-Rufa’i.
Ya ƙara da cewa ” Rotimi Amaechi ya yi takarar shugaban ƙasa kuma ƙila yana son ya sake yi, Atiku Abubakar ya sha yin takarar shugaban ƙasa haka nan Peter Obi ya yi takarar shugaban ƙasa.
“Mun yi wa kanmu faɗa cewa ya kamata mu ajiye wannan maganar, mu kafa jam’iyya ƙaƙƙarfa… duk mai buri, a zo a bi ƙa’idojin jam’iyya, duk wanda Allah ya zaɓa a mara masa baya.”
Haɗakar Daɓid Mark da Atiku bai shafi muƙamin PDP ba, inji jam’iyyar:
Jam’iyyar Peoples Democratic Party ta bayyana cewa har yanzu ba ta yanke wani hukunci a hukumance ba dangane da yunƙurin haɗakar 2027 da ke neman ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu.
A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, Sakataren Yaɗa Labarai na Jam’iyyar PDP, Debo Ologunagba, ya ce a halin yanzu jam’iyyar ta maida hankali ne kan shirye-shiryen babban taronta na ƙasa mai zuwa.
Jam’iyyar PDP dai na fama da rigingimun cikin gida tun bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda ya ƙara tsananta a shekarar 2024 bayan taƙaddamar muƙamin Sakataren Jami’iyyar na ƙasa.
A ƙarshe dai an warware batun ne a madadin Samuel Anyanwu yayin taron Kwamitin Zartarwa na jam’iyyar karo na 100 da aka gudanar a ranar Litinin.
Duk da wannan ƙudurin, jam’iyyar ta shaida masu sauya sheƙa zuwa wasu jam’iyyun siyasa, inda wasu ‘ya’yan jam’iyyar suka yi mubaya’a ga sabuwar ƙawance da jam’iyyar ADC ke jagoranta.
Tun da farko dai, a ranar 15 ga watan Afrilu, gwamnonin jam’iyyar PDP a birnin Ibadan na jihar Oyo, sun bayyana cewa jam’iyyar ba za ta shiga duk wata haɗakar da ke da nufin ƙalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
Dangane da haka, kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na ƙasa a ƙarƙashin jagorancin muƙaddashin shugaban jam’iyyar na ƙasa, ya nanata cewa duk da cewa jam’iyyar a shirye take ta karɓi waɗanda suka sauya sheƙa daga wasu jam’iyyu, ba ta da sha’awar shiga jam’iyyar.
Sai dai kuma wannan matsayi ya sha banban da abin da jiga-jigan jam’iyyar PDP irinsu tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon shugaban majalisar dattawa, shugaban riƙon ƙwarya na ADC, Daɓid Mark, da tsohon gwamnan Jigawa Sule Lamido suka yi, waɗanda suka yi kira ga ‘yan jam’iyyar da ‘yan Nijeriya da su marawa gamayyar jam’iyyar ADC da ta kunno kai.
An yi wannan kiran ne ta wata sanarwa da Mark ya sanya wa hannu bayan wani taron dabarun hadin gwiwa da aka yi ranar Talata a Transcorp Hilton da ke Abuja.
Yayin da wasu daga cikin shugabannin suka fice daga PDP, wasu kuma sun nuna aniyar haɗa kai da ADC yayin da suke ci gaba da zama a jam’iyyar.
A martanin da ya mayar, muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na kasa Umar Damagum ya dage cewa jam’iyyar ta ci gaba da kasancewa a cikinta, ya kuma yi gargaɗin cewa za a dauki matakan ladabtarwa a kan ‘ya’yan jam’iyyar da ke yunƙurin kawo cikas ga jam’iyyar.
’Yan Majalisar Wakilai bakwai sun fice daga PDP da YPP zuwa APC:
’Yan Majalisar Wakilai bakwai daga jam’iyyun adawa a jihar Akwa Ibom sun koma jam’iyyar APC mai mulki.
Shida daga cikin ‘yan majalisar sun koma APC ne daga jam’iyyar PDP yayin da mamba ɗaya ya fice daga jam’iyyar YPP zuwa APC.
Kakakin majalisar Abbas Tajudeen ne ya karanta wasiƙunsu na sauya sheƙa ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar ta Akwa Ibom a majalisar, Unyime Idem a zauren majalisar a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin zaman majalisar.
’Yan majalisar da suka sauya sheƙa sun haɗa da Alphonsus Uduak, da Martin Esin, da Paul Ekpo, da Okpolupm Ette, da kuma Bassey Okon—dukkan su daga PDP — da Emmanuel Ukpong na jam’iyyar YPP.
A cikin wasiƙun nasu, ‘yan majalisar sun ce matakin nasu ya biyo bayan tuntuɓar da suka yi da ‘yan mazaɓar kuma ya samo asali ne sakamakon ƙara ruruwar wutar rikici a cikin jam’iyyunsu. Idem, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar kan harkokin kasuwanci, ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar PDP ne bayan ya shafe shekaru 26 yana aiki saboda taɓarɓarewar harkokin shugabanci, musamman kan ofishin sakataren ƙasa. Ya kawo misali da sashe na 68(1g) na Kundin Tsarin Mulki don tabbatar da sauya sheƙarsa.
Haka zalika, Martin Esin ya ce a hukumance ya fice daga jam’iyyar PDP a ranar 17 ga watan Yuni ya koma jam’iyyar APC domin biyan buƙatun ‘yan mazaɓar sa.
Ficewar tasu ba za ta rasa nasaba da sauya sheƙa ta siyasa da Gwamna Umo Eno ya yi ba, wanda ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a watan Yunin 2025.
“Bayan kammala zagaye na tuntuɓa a matsayina na bawanka, don haka na yanke shawarar komawa jam’iyyar APC gaba ɗaya,” inji gwamnan.
“Ba wai mun koma APC ne daga rauni ba, muna komawa APC ne daga matsayi mai ƙarfi.”
Eno ya ce, ya yanke shawarar komawa jam’iyyar APC ne domin cikakken goyon bayan sake fasalin tattalin arzikin shugaban ƙasa Bola Tinubu.
A baya dai gwamnan ya shaidawa kwamishinonin sa da waɗanda aka naɗa su su biyo shi APC ko kuma su yi murabus daga muƙamansu.
A halin da ake ciki, da yake mayar da martani, shugaban marasa rinjaye Kingsley Chinda, ya bayyana damuwarsa kan illolin sauya sheƙar, yana mai gargadin tasirinta ga dimokuraɗiyyar Nijeriya.
Ya amince da ‘yancin ’yan majalisa na ‘yancin yin tarayya a ƙarƙashin sashe na 40 na kundin tsarin mulkin ƙasar amma ya buƙaci shugaban majalisar da ya yi aiki da kundin tsarin mulki ta hanyar ayyana kujerun da abin ya shafa.
ɓangaren Abure ya ba Peter Obi sa’a 48 ya bar jam’iyyar Labour:
ɓangaren Julius Abure na Jam’iyyar Labour (LP) ya ba Peter Obi wa’adin sa’o’i 48 ya yi murabus daga jam’iyyar saboda alaƙarsa da jam’iyyar haɗaka ta ADC da Daɓid Mark ke jagoranta.
Mai magana da yawun ɓangaren, Obiora Ifoh, a wata sanarwar da ya fitar ya ce jam’iyyar ba za ta yarda Obi ya haɗe da wata jam’iyya ba yayin da yake memba a Labour Party.
Sanarwar ta ce, jam’iyyar ba ta goyon bayan mutane masu manufofi biyu ko masu yaudara, kuma duk wanda ke son ya goyi bayan jam’iyyar ADC ya yi murabus cikin sa’o’i 48.
ɓangaren Abure ɗin ta ce waɗanda ke cikin jam’iyyar haɗaka ’yan siyasa ne masu son dawowa mulki ta kowanne hali.
Ifoh ya yi zargin cewa Obi ya yi ta ganawar sirri da wasu ’ya’yan ƙungiyar domin jan hankalinsu su shiga ƙungiyar.
“Muna sane da wasu tarurrukan dare da aka yi tsakanin Peter Obi da wasu mambobinmu, inda suke neman su shiga cikin sabuwar jam’iyyarsa. Muna kuma sane da cewa da dama daga cikinsu sun ki sauya sheƙa da shi,” inji shi.
“Jam’iyyar Labour ta ci gaba da cewa ba ta cikin jam’iyyar, don haka, duk wani dan jam’iyyarmu da ke cikin jam’iyyar ana ba shi sa’o’i 48 da ya yi murabus daga mukaminsa na jam’iyyar a hukumance.
“Jam’iyyar Labour ba ta samuwa ga mutanen da ke da manufa biyu, masu yaudara, jam’iyyar ba za ta amfana da wadanda ke da kafa ɗaya a jam’iyya daya da wata kafa a wani waje ba.
“Mutanen da da safe suke ikirarin suna jam’iyyar Labour da yamma suna cikin kawance.
“Kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya matasa ne da suka gaji da tsohon tsari, sun gaji da yanke hukunci kan makomarsu.
“Sabuwar Nujeriya da matasa ke mafarkin ba ita ce abin da za a iya tabbatawa daga abin da muke gani a cikin ƙawancen ba.
“Wazannan mutane ‘yan siyasa ne masu son ra’ayi waɗanda kawai ke da sha’awar sake dawo da kansu cikin da’irar mulki – mutanen da ke da burin ci gaba da riƙe madafun iko.”
El-Rufa’i ya zargi APC da yunƙurin kawo ruɗani a haɗakar ADC:
Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana cewa gamayyar jam’iyyun adawa a halin yanzu da ke yin gangami a ƙaraashin jam’iyyar ADC na iya yin rijistar sabuwar jam’iyyar siyasa gaba ɗaya gabanin zaɓen 2027 a matsayin wata dabara ta murƙushe jam’iyyar APC.
El-Rufai ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa ta musamman da Sashen Hausa na Rediyo Faransa (RFI) a daren ranar Larabar da ta gabata, kan abin da ya bayyana a matsayin “Yunƙurin jam’iyyar APC mai mulki na kutsawa cikin jam’iyyar ADC, jam’iyyar da ta fi fice kwanan nan a matsayin haɗaɗɗiyar dandalin ‘yan adawa.
“Mun san APC za ta iya kutsa kai cikin ƙawancenmu,” inji El-Rufai.
“Shi ya sa muke da wani shiri a ajiye, idan suka yi nasarar haifar da hargitsi a ADC, za mu yi hijira zuwa wata jam’iyya.”
Tsohon gwamnan, wanda ya fito a matsayin ɗaya daga cikin waɗanda suka tsara sake fasalin jam’iyyar adawa, ya zargi jam’iyyar APC da yin amfani da dabarun karas da sanda: jawo hankalin ‘yan adawa da naɗe-naɗen muƙamai, ko ba da kuɗi, ko tikitin jam’iyya ta kai-tsaye, yayin da ta yi barazana kai waɗanda suka bijirewa buƙatunta wajen hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa kamar EFCC da ICPC.
A cewar El-Rufai, gwamnatin tarayya ƙarƙashin jam’iyyar APC na amfani da wasu habyoyi wajen tursasa ‘yan siyasa su shigo cikin ta, ko kuma a gurgunta su a zaɓe mai zuwa.
“Za su tono tsofaffin ‘yan jam’iyyar ADC tare da tunzura su da su yi watsi da ƙawancen a bainar jama’a. Wannan wani ɓangare ne na shirin haifar da rikice-rikicen cikin gida da kuma mayar da jam’iyyar maras tasiri a gare mu,” inji shi.
Duk da bayyana jam’iyyar ADC a Abuja a matsayin babbar motar ‘yan adawa a kwanakin baya, kalaman El-Rufai na nuni da cewa shugabannin gamayyar sun nuna shakku kan ɗorewar duk wata jam’iyya da za a iya amfani da ita daga cikinta.
Ya kuma yi zargin cewa jam’iyyar APC na ɗaukar nauyin rigingimun cikin gida a manyan jam’iyyun adawa kamar PDP, Labour Party, da NNPP a ƙoƙarin da suke yi na wargaza tasirinsu gabanin zaɓe mai zuwa a 2027.
“Abin da APC ke yi ba dimokuraɗiyya ba ne, zagon ƙasa ne na siyasa,” inji El-Rufai.
