Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya kai ziyarar ta’aziyya ga dangin marigayi Alhaji Aminu Ɗantata a gidansa da ke Kano, tare da rakiyar Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Mataimakin Shugaban Ƙasa ya bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa kuma mai tallafawa al’umma, Alhaji Ɗantata, a matsayin babban rashi ga ƙasa.
Alhaji Aminu Ɗantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a Abu Dhabi, Ƙasar Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan kasuwa masu taimakon jama’a a Nijeriya.
Marigayi Ɗantata, ya gina harkokinsa ne bisa tubalin kasuwancin da mahaifinsa ya shimfiɗa, inda ya zama ɗaya daga cikin sanannun ƴan kasuwa a tarihin Najeriya, yana da hannun jari a fannonin gine-gine, masana’antu, banki, noma da kuma man fetur.
A yayin ziyarar, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya bayyana alhinin sa bisa rasuwar Alhaji Ɗantata, yana mai cewa,
“Ba wai shugaba ne kawai muka rasa ba, mun rasa wata babbar cibiyar tarihi da ba za ta iya samun wata ba.”
Ya yabawa marigayin da irin hidimar da ya yi wa al’umma a rayuwarsa, yana mai cewa:
“Shi gada ne da ke haɗa mu da tarihimmu.”
Ya kuma yi addu’ar Allah ya jiƙan marigayin da rahama, ya kuma sa ya samu gidan Aljanna Firdaus.
Shugabanni da dama sun yi ta’aziyya dangane da rasuwar Alhaji Ɗantata, ciki har da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar. Sun bayyana rasuwarsa a matsayin babban rashi ga ƙasa, tare da yabawa da irin gudummawar da ya bayar ga ci gaban tattalin arzikin Nijeriya.
Gado ko tarihin Alhaji Aminu Ɗantata ya wuce kasuwanci kaɗai ya shahara wajen ayyukan jin ƙai, tallafa wa makarantu, masallatai, cibiyoyin lafiya, da kuma mata marayu da marasa ƙarfi a faɗin Nijeriya.
Kazalika tasirinsa a rayuwar tattalin arziki da zamantakewar ƙasar za a ci gaba da tunawa da shi har zuwa shekaru masu zuwa.
