Daga JAMILU GULMA, a Kebbi
Al’ummar yankin garuruwan Libata da Lokon-Uba da Kabiriba da sauran ƙananan ƙauyuka da ke ƙaramar Hukumar Mulki ta Ngaski da ke Jihar Kebbi sun koka bisa ga yadda kamfunnan haƙar ma’adanai a yankin ke cin karen su ba babbaka yayin da aka mayar da al’ummomin yankin ’yan kallo ba tare da wani ihsani ba ko samar da abubuwan more rayuwa ba.
Malam Sani Aliyu daya ɗaga cikin matasan yankin kuma mai sana’ar kabu-kabu (acaba)ya bayyana wa wakilinmu cewa, waɗannan mutanen sun daɗe suna cin karen su ba babbaka a yankin wajen haƙar ma’adanai da su ke yi ba kakkautawa sai dai mazauna garuruwan da ke zagaye da inda a ke haƙar ma’adanai ɗin ba wani abu da suka amfana da shi sai dai ƙura da manyan motocin su ke barbaɗa musu ba dare ba rana kuma suna lalata titunan da mutanen su ke sufuri na yau da kullum musamman a irin wannan lokacin na damina.
Ya ƙara da cewa, ya kamata aƙalla a ce an ɗauki matasan garuruwan da ke zagaye da wuraren ayyuka daban-daban amma a maimakon haka sai dai su zo da ma’aikatan su daga waɗansu sassan ƙasar nan da kuma waje duk da ya ke al’ummar yankin suna sane da cewa kamfanin yana ɗibar arzikin yankin na billiyoyin kuɗi a kowane sati fiye da yadda hankali ke ɗauka ba tare da wani abu na amfani kamar asibiti, makarantu tituna ko wani abu na more rayuwa da suka yi saɓanin yadda ya ke a dokokin kafa kamfunna.
Wani direba mai suna Muhammad Ali da ke sufuri a wannan yankin ya nuna damuwarsa bisa ga yadda manyan motocin kamfanin da ke karakaina a kan hanyoyin ke jefa su cikin matsala sanadiyyar lalata hanyoyi da su ke yi wanda da yawa idan aka yi rashin sa’a wata mota ta maƙale sai a wuni ana wahala sai dai su ba ta shafar su saboda motocin su suna da ƙarfin da su ke iya ratsa gonakin mutane suna wucewa.
Alhaji Yakubu wani dattijo da ke da gona a kan hanya ya koka bisa ga yadda manyan motocin kamfanin suka mayarda gonakin su ko’ina hanya wanda shi ne yanzu suka ɗauki matakin saro manyan itace suka yi shinge don hana bi ta cikin gonakin su.
Ya ce, sun ɗauki matakin haƙa manyan ramuka ko kuma saro manyan itace suka su saka a gefen gonakinsu ne saboda su kare amfanin gonar su daga manyan motocin da ke buɗe hanyoyi ko’ina cikin gonakinsu.
ɗaya daga cikin ma’aikatan kamfanin Mufkad Mines and Inɓestment Limited da bai so a bayyana sunansa ba ya bayyanawa wakilinmu da cewa, rashin aiki ne ya sanya su aiki a wannan kamfanin saboda bambancin su da bayi ba yawa, tun kama daga yadda ake bautar da su wajen aikin zuwa wajen kwanan su abin sai wanda ya gani.
Na farko dai ba wata takarda ta shaidar ɗaukar su aiki wanda shi ne ya ke bai wa manyan jami’an kamfanin damar korar su daga aiki a duk lokacin da aka ga dama ba tare da wata wahala ba saboda babu wata yarjejeniya, haka-zalika bayan wahalar aikin babu albashin a zo a gani.
Haka zalika yanzu haka sun fifita ‘yan ƙasashen waje (Yan Chana) a kan ‘yan Nijeriya saboda yanzu haka idan ka je wajen kwanan ‘yan Chana ɗin nan za ka ga irin yadda aka ƙawata shi duk da kasancewar wajen cikin daji ne za ka sha mamaki saboda komai na more rayuwa akwai amma a wajen kwanan Yan Nijeriya har da wuta babu ballantana banɗaki ko wani abin amfani mai kyau duk da irin aikin wahalar da suke yi.
“Mun sani waɗannan mutanen suna amfani ne da mu suna samun maƙuddan kuɗaɗe wannan albarkatun ƙasa saboda ƙoƙarin mu da kuma sanin yanayin irin wannan aikin kuma muna ba su haɗin kai kamar yadda suke buƙata, amma sai dai mu suna zalintar mu wajen biyan mu haƙƙoƙanmu yadda ya kamata,” inji shi
Wakilin Blueprint Manhaja ya yi tattaki zuwa kamfanin MUFKAD Mines and Inɓestment Limited ɗaya daga cikin kamfunnan da ke haƙar ma’adanai a kusa da garin Libata, inda ya tarar ana ta haƙar ma’adanai ba ƙaƙƙautawa kuma ya nemi jin ta bakin ɗaya daga cikin shugabannin kamfanin da suka haɗa da Alhaji Muhammad Lawal ko kuma Manajan Darakta Blessing chike.
ɗaya daga cikin yaransu mai suna Adams ya bayyana cewa, dukkansu ba sa nan sannan kuma shi ba ya da hurumin magana da ‘yan jarida amma dai shi a iya sanin sa ba su da wata matsala da kowa.

Wakilin Blueprint Manhaja ya nemi jin ta bakin shugaban ƙaramar Hukumar Mulki ta Ngaski Honarabul Maniru amma dai hakan ba ta samu ba saboda ba ya gari kuma lambar sa ba ta shiga ya tura saƙo, amma dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba amsa.
Waɗansu bayanai da wakilinmu ya tattara daga yankin sun nuna cewa, ana hasashen da yawa daga cikin masu haƙar ma’adanai ɗin suna yin aikin ne ba bisa ƙa’ida ba saboda ba su da lasisi ko kuma suna lasisin jabu ne ko kuma suna wuce ƙa’idojin gudanarda aikin saboda akwai wani shiri ne tsakanin su da mahukumta da masu iko wanda yanzu haka an rufe kamfunnan haƙar ma’adanai da dama a wannan yankin sanadiyyar waɗansu dalilai daban-daban.
Haka zalika ya nemi jin ta bakin Hukumar Harkokin Ma’adanai ta Jihar Kebbi sai dai wayar Babban Sakatare a ma’aikatar Alhaji Bello Yahaya Geza ba ta zuwa kuma ya aika saƙon kar ta kwana amma dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba amsa.
Sai dai darakta a sashen ma’adanai Malam Ibrahim Tanimu ya ce, shi ma ba shi da hurumin magana da manema labarai ba tare da iznin shugabannin sa ba saboda aikin gwamnati ana yin sa ne bisa ga tsarin da doka ta tanada.
