‘Yan Majalisar Katsina sun gabatar da kuɗirin gaggawa kan matsalar tsaro a jihar

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

‘Yan majalisar dokokin Katsina sun bayyana damuwa kan ƙaruwan ayyukan ‘yan bindiga a yankuna da dama na jihar, duk kuwa da sulhun da aka yi dasu.

Majalisar dokokin Katsinan ce ta bayyana damuwa kan yadda tsaron ke ƙara taɓarɓarewar a zamanta na Larabar nan, wanda shugabanta Hon. Nasir Yahaya-Daura ya jagoranta.

Yayin zaman ne, ɗan majalisa mai wakiltar ƙaramar hukumar Dutsinma, Alhaji Muhammad Abubakar Khamis ya gabatar da ƙudirin da ke buƙatar ɗaukar mataki na gaggawa.

Abubakar Khamis ya yi kira ga gwamnatin jihar a kan ta ƙara zage damtse wajen yaƙi da matsalar tsaron , ta hanyar samar da dakarun soji da sauran jami’an tsaro a yankin da yake wakilta saboda ta’azzarar hare-haren ‘yan bindiga a ‘yan kwanakin nan.

Ɗan majalisar wanda shi ne shugaban kwamitin tsaro na majalisar, ya jaddada cewa al’ummar yankin na rayuwa cikin tsoro da fargaba, lamarin da ke buƙatar ɗaukin gwamnati musamman ta tarayya.

Ya ce akwai buƙatar ƙarin jami’an tsaro a Maƙera, Gammo, Karofi da Dabawa na ƙaramar hukumar Dutsinma.

Jihar Katsina na daga cikin jihohin Arewacin Najeriya da hare-haren ‘yan bindiga ke ci gaba da addabar mutane, ta hanyar hana su rayuwa cikin kwanciyar hankali da zaman lafiya, gami da fargabar zuwa gonaki don noma.

By ukarofi