
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sanata, Dino Melaye, ya bar babbar jam’iyyar adawa ta PDP sakamakon nuna gazawarta ta ceto Nijeriya daga halin taɓarɓarewar harkokin siyasa da ta tsinci kanta a ciki, kamar yadda ya bayyana.
Dino Malaye, wanda tsohon sanatan mazaɓar Kogi ta Yamma ne, ya faɗi haka ne a ranar Alhamis, a wani rubutu ta kafar X, inda ya sanar da shugaban jam’iyyar na Gunduma ta 1 dake Aiyetoro Gbede a Ƙaramar Hukumar Ijumu ta jihar batun ficewar tasa.
A saƙon, wanda ke ɗauke da kwanan wata kamar haka: 4 ga Yuli, 2025, Melaye ya ce matakin abu ne mai muhimmanci duba da yadda jam’iyyar ta gaza share wa ƴan Nijeriya hawaye daga ƴan siyasar da suke hana ruwa gudu a harkokin ƙasar.
Ɗan takarar gwamnan a zaɓen 2023 ya bayyana cewa, bayan dogon nazari game da halin da jam’iyyar take ciki, ya ga dacewar janyewa ko bada gudunmuwarsa ga harkokinta.
Ya kuma yi godiya bisa yadda jam’iyyar ta ba shi damar yi wa al’umma aiki a ƙarƙashinta a yayin da ya ke mamba.
Ana ganin hakan a matsayin wani ɓangare na shirin tunkarar babban zaɓen 2027.
A kwanan nan tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar.
