Akasarin matsalar tsaro a Katsina daga garuruwa suke faruwa, inji kwamishinan tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro Dr Nasiru Mu’azu Ɗanmusa ya bayyana haka da yake hira da manema labarai a gidan Gwamnatin Katsina.

Ya ce duk yawancin kayyakin da ‘yan bindiga ke amfani da su wajen aikata ta’addanci daga garuruwa ake kai masu.

Dr Ɗanmusa ya bada misali da man fetur da yace ana kai masu a maɓoyan su a da daji kan kowane litan mai ɗaya ana sai da masu a kan Naira 3000.

Haka ma baburan hawa da suke amfani da shi,kayan abinci,lemun ƙwalba,bindigogi, harsashi, miyagun ƙwayoyi da rigar sojoji duk daga gari ake saida masu.

Kwamishinan ya ƙara da cewa ‘yan bindiga da ke zaune a daji bai san wane ne mai arziki,ɗan kasuwa sai mutanen gari sun faɗa masu.

Domin haka yayi kira ga al’umma da su tashi tsaye wajen bada tasu gudunmawa ta hanyar bada bayanai na sirri kan yadda za a shawo kan matsalar tsaro a jihar.

Kwamishinan ya bayyana cewa ya zama wajibi al’umma su haɗa kai da jami’an tsaro wajen lalubo hanyoyi da za a bi a kawo ƙarshen ta’addanci a jihar.

Ya kuma miƙa ta’aziya a madadin gwamnatin Dikko Raɗɗa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu sakamakon hare haren yan ta’adda a jihar.

Dr Ɗanmusa ya jaddada ƙudirin gwamnatin Dikko Raɗɗa na cigaba da yaƙi da ta’addanci a jihar, wanda a kan haka ya nemi ya sanar da cewa gwamnatin jihar za ta ƙara ɗaukar jami’an tsaron CWC aiki domin ƙara samar da tsaro a jihar.

By ukarofi