Anyi kira ga Gwamnatin Tarayya ta dawo teburin tattaunawa da jami’an kiwon lafiya

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Kwamred Mannir Suleiman mamba na ƙungiyar jami’an kiwon lafiya na manyan makarantun harkokin lafiya ta ƙasa yayi wannan kira.

Ya nuna damuwarsa game da yajin aikin na gargaɗi da yace ya jefa marasa lafiya a asibitoci na gwamnatin tarayya a Katsina da Daura cikin mawuyacin hali.

Kwamred Suleiman wanda tsohon shugaban ƙungiyar ma’aikatan kiwon lafiya reshen Jihar Katsina ya zargi gwamnatin tarayya da karya alƙawari da tayi da ma’aikatan.

“Gwamnatin tarayya ta gaza biyan sabon albashi na Naira dubu 70 da ma’aikatan,mai makon haka sai ta ce dubu 40 za su biya wanda wannan rashin adalci ne,”inji kwamred Suleiman.

Ya bayyana cewa akwai wasu alawus alawus alawus da suka daɗe har yanzu gwamnatin ta gaza biya babu wani bayani shiyasa ƙungiyar ta ɗauki wannan mataki na yajin aiki na gargaɗi.

Kwamred Mannir Suleiman wanda harwala yau shugaban ƙungiyar haɗin kan Funtua ya jawo hankalin gwamnatin tarayya da ta sani mafi yawan ma’aikatan kiwon lafiya ba yan jihar da suke aiki bane kuma basu da iyalai.

Asibitocin gwamnatin tarayya guda na garin Daura da Katsina ya shafa a jihar waɗanda ‘yan uwan marasa lafiya suka janye mutanen su.

Halin da ake ciki wata ƙungiyar abokan asibiti ƙarƙashin jagorancin Alhaji Bilya Sanda take bada agajin gaggawa a babban asibitin gwamnatin tarayya da ke garin Katsina

By ukarofi