Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
’Yan bindiga sun tarwatsa ƙauyuka sama da 10 da ke zagaye da ƙaramar hukumar Bakori ta jihar Katsina sannan suka mayar da sama da 6,000 ’yan gudun hijira.
Maharan dai sun riƙa kashe mazauna ƙauyukan sannan su sace wasu su yi garkuwa da su domin karɓan kuɗin fansa.
Bayanai na cewa a ’yan kwanakin nan, ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka tarwatsa ƙauyuka kamar su Guga da Kandarawa da Kakumi da kuma Monono.
Har ila yau lamarin ya shafi ƙauyukan anguwar ’Yar Dabaru da anguwar ɗan Marka, da Sabon Gida da ƙauyan Doma da dai sauransu.
Hakan dai ya haifar da ƙauracewa ƙauyukan ga mazaunansu da suke da sauran numfashi inda a yanzu haka ake da ’yan gudun hijira sama da 3,500 da ke neman mafaka a cikin garin Bakori.
Kazalika, rahotanni sun kuma ce akwai wasu sama da 2,500 da ke garin Guga don neman mafaka.
’Yan gudun hijirar waɗanda akasarinsu mata ne da ƙananan yara sun watsu a wurare daban-daban.
Manhaja ta zagaya unguwan Kafaɗi da unguwar Ma’aru da ke Sabuwar Abuja a cikin garin na Bakori, inda wakilinmu ya tarar da cincirindon mata da ƙananan yara a rakuɓe, a gidajen ’yan uwa, wasu kuma a makarantun firamaren gwamnati da ke ƙaramar hukumar ta Bakori.
A tattaunawar Wakilinmu da wasu daga cikin ’yan gudun hijira waɗanda suka fito daga ƙauyaku daban-daban na jihar, sun nuna alhininsu game da yadda ’yan bindigar ke cin karensu ba babbaka a yankin.
Imrana Shafi’u wanda ’yan bindigar suka harbe shi a ƙafa har wuri biyu, wanda shi ya yi hijira ne daga kauyan ɗan Marka, ya ce lamarin na da ban tsoro matua.
A cewarsa, “Ni ma Allah ne ya sa zan rayu domin ’yan bindigan sun zaci na mutu ne.
“Domin da suka zo kanmu harbin kan mai uwa da wabi, suka yi ta yi, inda suka kashe mutane da dama.
“Ni ma dai Allah ne ya tsirar da ni, domin duk waɗanda nake tare da su duk an kashe su, ni kaɗai na tsira cikin ikon Allah,” inji shi.
Ita kuwa Malama Marawiya wacce ta yi gudun hijira daga ƙauyan ’Yar Dabaru ta ce da rana tsaka ’yan bindiga suka keto cikin ƙauyan nasu, suka tarwatsasu sa’ilin da suka tasa ƙeyar mata sama da 10 kuma duk yawancinsu suna ɗauke da goyo suka yi cikin daji da su.
Marawiya ta ƙara da cewa kusan kwanakin matan 10 ke nan a hannun su kuma sun ce sai an biya kuɗin fansa har Naira miliyan ɗaya da rabi kan kowanne mutum ɗaya kafin a sake su.
Ta ƙara da cewa “A da in suka ɗauki mutum bai wuce su ce a ba su Naira dubu ɗari biyar ba amma a wannan karon sai suka ce sai an biya har sama da naira miliyan ɗaya da rabi ga kowanne mutum,” inji ta.
Yusuf Usman, wanda suka yi sansani a wata makarantar firamare ta Nadabo da ke cikin garin Bakori, ya ce kusan su ɗari uku ne suka yi gudun hijira daga ƙauyan Doma, cikinsu har da tsofaffi.
Ya kuma ce, “A haka muka tako da afa muka yini muna tafiya tare da mata da yaran ƙanana har Allah ya kawo mu garin Bakori,” inji shi.
Ya ƙara da cewa kusan shekara biyar kenan suna fama da wannan matsalar ta tsaro, kuma ba dare ba rana bare damina ko rani, haka ake shigowa ƙauyakun su ana kashe su sannan kuma a tasa ƙeyar su a tafi da su daji domin karɓan kuɗin fansa.
Shugaban kwamitin da ƙaramar hukumar Bakori ta kafa domin kula da ’yan gudun hijirar, Malam Mamman Yaro Bakori, ya ce adadin ’yan gudun hijirar sun kai 3,500 a garin Bakori.
Ya ƙara da cewa a garin Guga kuma akwai aƙalla kimanin mutane 2,500 da suke gudun hijira a can.
Shugaban ya ce kuma kusan a kullum yawan su aruwa yake yi, sannan suna warwatse ne a wurare daban-daban a inda wasu suke zaune a gidajen ‘yan uwansu wasu kuma suna zaune ne a makarantar firamare ta Nadabo a cikin garin Bakori.
Sai dai ya ce tuni Shugaban ƙaramar hukumar Bakori, Abubakar Barde ya bayar da umurnin kai masu tallafin kayan abinci sau uku a rana tare da kuɗin cefane don sauƙaƙa masu rayuwar da suke ciki.
Wasu na bayyana cewa a ‘yan kwanakin nan ’yan bindigar na cin karensu babu babbaka a inda suka kafa sansaninsu a dajin Guga da Kandarawa da Kakumi.
