Yadda uwargidan shugaban ƙasa ta ba da gudunmawar biliyan N15 cikin shekaru biyu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

A wani abin da ake ganin ya zama tarihi na karimci da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin siyasar Nijeriya, uwargidan shugaban ƙasa, Sanata Oluremi Tinubu, ta ba da gudunmawar sama da Naira Biliyan 15 ga waɗanda bala’o’i, iyalai da suka rasa matsugunansu, zawarawa, mata, da kuma tsofaffi a cikin shekaru biyu kacal ta hanyar aikin ‘Renewed Hope Initiatiɓe’ (RHI).

A ranar Talata, 29 ga Yuli, 2025, ta sake fitowa fili yayin da ta sanar da bayar da gudunmawar Naira Buliyan 1 a jihar Benuwe, wanda aka yi niyya ga waɗanda harin Yelewata ya shafa, inda aka kashe sama da rayuka 100 a watan Yuni.

Da take jawabi a sabon ɗakin taro na gidan gwamnatin Benuwe, ta sake jaddada ƙudirinta ga marasa galihu, ta ce, “manufarmu ita ce dawo da fata, sake gina rayuka, da sabunta Nijeriya.”

Wannan gudunmawar ita ce ta baya-bayan nan a cikin jerin gudunmawar da ta bayar wanda suka yi tasiri ga rayuwar al’umma. Daga Borno zuwa Filato, Legas zuwa Saliyo, ofishinta duk da rashin amincewa da tsarin mulki ko kasafin kuɗin da doka ta tanada, ta tura wasu maƙudan kuɗaɗe don bayar da agaji, galibi cikin kwanaki da iftila’i.

Binciken gudunmawar da aka bayar a ƙarƙashin Remi Tinubu tun lokacin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya hau kan karagar mulki a watan Mayun 2023 ya nuna cewa RHI ta zama ƙungiya mai zaman kanta da ke ƙarƙashin jagorancin uwargidan shugaban ƙasa da ta fi bayar da tallafi a zamanin mulkin dimokraɗiyyar Nijeriya:

Biliyan N1 ga waɗanda hare-haren ƙabilanci ya shafa a jihar Filato (Yuli 3, 2025).

Biliyan N1 zuwa Jami’ar Obafemi Awolowo, Ile-Ife (Oktoba 10, 2024)

Biliyan N1 ga Asusun Ciwon Daji na Nijeriya.

Biliyan N1 don tallafawa yunƙurin kawar da tarin fuka

An raba miliyan N950 ga sojoji 250 da suka yi ritaya daga aiki, ‘yan sanda da manyan ’yan ƙasa.

Miliyan N500 na agaji ga waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Borno.

Miliyan N427.75 ga zawarawa da marayun sojojin da suka mutu.

Biliyan N1.9 don tallafawa tsofaffi a faɗin jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya.

Naira miliyan 100 ga waɗanda fashewar tanka ta shafa a jihar Neja.

Miliyan N150 don gina asibiti a Saliyo ga ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje.

A Jihohin Benuwai da Filato kaɗai, ta ba da gudunmawar Naira biliyan 2 ga iyalan da suka rasa matsugunansu a cikin ƙƙsa da wata guda.

Idan aka kwatanta da magabata, gudunmawar Remi Tinubu ta yi tasiri matuƙa.

By ukarofi