Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Masanin Tattalin Arziki na Siyasa, Farfesa Pat Utomi, ya ce ya kamata Nijeriya ta sake inganta dabarun samar da wutar lantarki na Band A, yana mai cewa tsarin yana “tsotse” ’yan Nijeriya.
Masanin tattalin arzikin ya kuma shawarci majalisar dokokin ƙasar da ta mayar da hankali kan dokokin da za su ciyar da ’yan Nijeriya gaba fiye da ayyukan sa ido.
Utomi, wanda kuma shi ne Mai Gudanar na Big Tanti, ya yi wannan kiran a taron manema labarai na ƙungiyar kan “yanayin ƙasa” a ranar Litinin a Legas.
Band A yana nufin rukunin abokan cinikin wutar lantarki waɗanda ke samun mafi ƙarancin sa’o’i 20 na wutar lantarki a kowace rana.
Rabe-raben rukunin wani ɓangare ne na tsarin biyan kuɗin wutar lantarkin da Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta aiwatar.
Abokan ciniki a cikin Band A suna biyan mafi yawan farashin wutar lantarki saboda ingancin rukunin su.
Utomi ya bayyana rukunin Band A a halin yanzu a matsayin “hanyar tatsar mutane”.
“Misali malamin jami’a a Band A zai kashe kashi 75 na albashin sa akan kuɗin wutar lantarki kaɗai.
“Idan ba a hanzarta sabunta tsarin ba, wannan tsarin zai ƙara talauta ‘yan Nijeriya, musamman ma’aikata,” inji shi.
Dangane da dokoki, ya ce duk da cewa sa ido ya kasance wani muhimmin ɓangare na ayyukan majalisar dokokin ƙasar, bai kamata a ba shi fifiko kan dokoki ba.
A cewarsa, ya kamata majalisar dokokin ƙasar ta kammala duk wasu sauye-sauyen ƙasar tun kafin yanzu.
“Muna buƙatar sauye-sauye na gaskiya.
“Zai zama ɓarna ga Nujeriya idan al’ummar ƙasar za su shiga 2027 da tsarin mulkin aasa mara kyau.
“Bugu da ƙari, akwai fannoni kamar rashin tsaro da kuma samar da gyare-gyare ga aikin ‘yan sandan wanda ke ci wa kowa tuwo a kwarya a yayin da ake fuskantar munanan laifuka a Nijeriya.
“Yana da muhimmanci a ce Nijeriya ta karkata ayyukan ‘yan sanda ta yadda al’ummomi za su samu ‘yan sandansu masu ɗauke da makamai kamar yadda ya kamata a jihohi, baya ga ‘yan sandan tarayya.
“Wannan ita ce hanya mafi sauri yanzu don magance rashin tsaro.”
Ya ce, yanayin tsaro ya fi shafar jama’a, inda ya nuna cewa mutanen karkarar Nijeriya fuskantar matsalar.
