Wajibi ne kowannen mu ya yi iya ƙoƙari wajen kare martabar Ma’aikin Allah – Da’iratuh Shurafa’u

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugaban ƙungiyar Da’iratuh Shurafa’u  Malam Sharu Aminu Salga wanda akafi sa ni da Baba Sharu  ya bayyana cewa wajibi ne alummar musulmi ko da ga wacce ƙungiya kake ko fahimta ta addini to wajibi ne ka fito ka bayyana goyan bayanka wajen kare martabar maaikin Allah Annabi Muhammadu Alahimmusalatu Wassalam domin kuwa wajibi ne mu akan mu mu kare martabar maaikin Allah da ahalinsa wanda bazamu yadda wasu mutane su dinga maganganu akan maaikin Allah ba yadda suka gadama ba kuma abin takaici shi ne anyi irin wannan a Bauchi wanda wani yace baya neman taimakon maaikin Allah wa iya zibillah mu dai muna taimakon Allah duniya da lahira wannan kuma shi ta shafa ba mu ba da sauran maganganu wanda in aka faɗa a wannan wuri kowa sai yayi kuka saboda munin su Allah ya kiyaye kuma can Allah ya ɗaukaka ya ƙare martabar maaiki mu soyayya ce gareshi ta sa muke wannan kamar dai yadda Baba Sharu shugaban Da’iratuh Shurafa’u a wani gagarumin taron da Da’iratuh Shurafa’u ta gabatar a ɗakin taron na gidan Mumbayya Gwammaja Kano a lokacin da ya gabata.

Ya ce kan nuna rashin yadda da cigaba da irin wannan maganganu daga waɗansu mutane yasa muka ɗau mataki na rubuta takarda da aikawa ga ɗaukacin hukumomi masu ruwa da tsaki tun daga kan Gwamna Kano da sauransu da kuma gidan Malamai na ɗariƙu daban daban kamar irin gidan Sheik Usman Zangon bare bari gidan ƙadiriyya da dai sauransu da muka aika domin ɗaukar mataki dai dai da sharia bamu da nufin fitowa muyi kona kone ko fashe fashe cikin tsari dai dai da sharia muke ɗaukar matakin mu amma bazamu yarda da cigaba da taɓa martabar maaikin Allah ba daga ko waye.

A ƙarshe ya ce wannan Daira ta shurafa’u ta shirye ta haɗa kai da duk wani musulmi wajen wannan gwagwarmaya domin maaikin Allah na kowa kuma rahama ce ga talikai har ma wand aba musulmi ba Manzon Allah gatan su ne don haka ko waye zamu haɗa kai dashi wajen kare martabar Ma’aikin Allah.

By ukarofi