Koyi da Gwamna Abba ya sa muke kiran Ciyaman ɗin Fagge gatan ilimi – Hon. Ibrahim Sallau

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Sakataren Ilimi na ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Malam Ibrahim Sallau Ibrahim, ya bayyana cewa yadda shugaban ƙaramar hukumar fagge Hon Salisu Usman masu ke yin koyi da gwamna Kano Abba Kabir wajen bunƙasa ilimi a kowani mataki shi ne yasa muke cewa shugaban ƙaramar Hukumar Mista Education ko kuma Gatan Ilimi domin kuwa makarantu firamare 246 da kuma ƙananan makarantun sakandare 51 na ƙaramar hukumar ba wacce bata san gwamna Abba yazo ba haka kuma babu wacce bata san Hon Salisu Usman Masu ne shugaban ƙaramar hukumar Fagge wannan kuma na da alaƙa ne da kowannen su ya damu da harkar ilimi gwamna a matakin jiha shugaban ƙaramar hukuma a matakin ƙaramar hukumar Fagge kamar dai yadda sakataren ilimi Malam Ibrahim Sallau ya bayyana.

Ya ce a watanin baya ne gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tara sakatarorin ilimi ƙarkashin shugabanin ƙananan hukumomi 44 na Kano aka raba musu ɗinbun litattafai a gidan gwamnatin wanda aka rabawa ɗalibai makarantun ƙananan hukumomin kyauta haka kuma gwamnan ya biyawa ɗalibai Neco kuɗin jarabawa na billyoyin nairori a nan jihar Kano abin a yabane.

A ƙarshe ya ce shi ma Hon. Salisu Usman Masu yanzu yana gina gine a makarantu ƙaramar hukumar a ko ina wasu ajujuwa da aka ga sunyi rauni maimakon gyara rushensu yasa akayi aka gina sababbi wannan kishin ilimi ne sai kuma wata ƙaramar sakandare da akin ginin ta yayi nisa da ake kira Mega School wacce ana tunanin babu irin ta a afrika wannan aiki koyi da Gwamnan Kano Abba da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa kwankwaso  wajen kishin ilimi da sauran fanonin rayuwar alummar kano.

By ukarofi