Ya kamata Gwamna Abba ya dinga zama da ƙananan ƙungiyoyi – Shugaban masu shayi na Kano

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

An bayyana cewa da a ce Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf zai ɓullo da tsarin zaɓo ƙananan ƙungyoyi na ƙasa waɗanda suke tare da jama’a 20 duk wata a zauna da su ko da wata uku ne a ce ana gayyato ƙungiyoyi daban-daban a ba su dama su bai wa gwamnatin shawara a basirar su da tunaninsu hakan zai kawo cigaba domin ɗan ƙanƙanin lokaci an zauna da ƙungiyoyi masu yawa har ma da manyan in ta kama duk da yake su ban sani ba ko ana zama da su amma dai ƙungiyoyi irin namu akwai buƙatar a yi hakan domin aiki da ƙungiiyoyi irin namu ya sa muka samu tallafi sana’a mu kimanin 5000 a zamanin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yana gwamnan Kano wanda muke so gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuna da masu shayi, abincin kowa a duniya, kamar dai yadda shugaban masu sayar da shayi na ƙasa reshen jihar Kano Shehu Sulaiman Muhammad Gadon ƙaya ɗan asalin Tsakuwa ƙaramar Hukuma Dawakin Kudu Jihar Kano.

Shugaban masu shayi Malam Shehu ya ce ya zaɓi sana’ar shayi ne ya bar aikin gwamnati domin cikin shekaru sama  da 35 da suka wuce ya kammalla makaranta aka kawo masa takardar aikin gwamnati wani kuma ya bashi shawara ya kama sana’ar shayi sai ya kama sanaar shayi ya hakura da aikin gwamnati yanzu yana da yara 11 da suke wannan sana’a ta sayar da shayi kuma ciki harda mai digiri mai daraja ta biyu (Second Class) da ya samu ABU Zaria kuma da wannan sana yak e ɗaukar nauyin ƙaratun su da taimakawa yan uwa da maƙota da sauran su a wannan sana’a da ta yi masa 19 ta arziki.

A ƙarshe ya ce a matsayinsu na masu sana’ar shayi masu sammako da kuma raba dare suna da kyakkyawar alaƙa da jami’an tsaro da kuma bada gudunmawa ta fuskar tsaro da taimakawa wajen hana shaye shaye da faɗace faɗace ta yadda wurarensu ya zama wuri samun abinci, muhawara, da ke kawo fahimtar juna a tsakanin matasa musamman in an taso daga wasan kwallo kuma akwai abubuwa da ya gani a tsakanin hanyar sa ta komawa gida da bazai manta ba duk da Allah ya ye masa tsoro nayin dare ko sammako.

By ukarofi