Zamfara: Yadda na san zirga-zirgar ’yan bindiga – Dauda

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMMAD

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal Dare, ya ce, ya san komai kan zirga-zirgar jagororin ’yan bindiga a jiharsa, yana mai cewa, za su zama tarihi idan har yana da iko kan hukumomin tsaro.

Gwamna Dauda, a cikin wani faifan bidiyo da ya yaɗu, ya bayyana cewa, ya san ainihin wuraren da ’yan bindigar suke ɓuya. Gwamna Dauda Lawal ya bayyana cewa, yana sane da ainihin wuraren da manyan shugabannin ’yan bindigan da ke addabar jihar suke.

Gwamna Dauda Lawal ya kuma koka kan yadda yaƙi da ‘yan bindiga ya ke kwan-gaba-kwan-baya a jihar. Ya bayyana cewa, duk da sanin motsin ’yan bindiga da hada-hadarsu, an kasa shawo kan matsalar ne, saboda shugabannin tsaro a Zamfara suna karɓar umarni ne kawai daga Abuja.

Gwamnan ya bayyana cewa, yana da masaniya kan duk inda shugabannin ’yan bindiga suke a jihar, amma ba zai iya yi musu komai ba.

Ya nuna cewa, ko fita suka yi zai sani amma ba yadda ya iya da su tun bai da iko kan hukumomin tsaro.

Gwamnan ya bayyana cewa hakan ya kan sanya ya zubar da hawaye, saboda ga matsala yana gani amma bai da ikon kawo ƙarshenta.

“Na rantse da Allah Maɗaukaki, duk inda shugaban ’yan bindiga yake a cikin Zamfara, na sani, kuma idan ya fita, na sani.”

Gwamna Dauda ya bada misali kan yadda ’yan bindiga suka taɓa kai hari a ƙaramar hukumar Shinkafi, amma jami’an tsaro a jihar suka ƙi tunkararsu saboda ba su samu izini daga Abuja ba.

“Akwai lokacin da ‘yan bindiga suka kutsa Shinkafi, aka sanar da jami’an tsaro, amma suka ƙi fita saboda kawai ba a basu umarni daga Abuja ba,” inji Gwamna Lawal

Ya jaddada cewa gwamnatinsa ta yi duk mai yiwuwa don tallafa wa hukumomin tsaro duk da cewa ba shi da ikon shugabanci a kansu kai tsaye.

“Ina yin hakan ne duk da cewa ba ni da iko a kan hukumomin tsaro, amma saboda nauyin da ke kaina na kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Zamfara,” inji Gwamna Dauda.

By ukarofi