Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Cibiyar gyaran idanu a Katsina mai suna Izala eye Foundation ta sami amincewa ta kammala aikin gyaran asibitin Ƙofar Durɓi da ke garin Katsina.
Shugaban ƙungiyar Izalatul bidi’a wa Ikamatul sunnah reshen Jihar Katsina Sheikh Yakubu Musa Hassan ya bayyana haka a wajen babban taro a cibiyar da ya gudana a Katsina.
Ya sanar da cewa Gidauniyar Sauttus sunnah da tallafawa marayu za ta kammala gyaran asibitin idanun.
Sheikh Musa Hassan ya ce idan an kammala gyare-gyaren zai ƙunshi sashin maza da na mata, ɗakin fiɗa da sashin gudanar da harkokin mulki.
Sauran sun haɗa da Masallacin Juma’a, makarantar islamiyya da gida Liman.
Malam Yakubu Musa ya bayyana cewa ita cibiyar an ƙirƙiro ne baya da cibiyar Al Basar Eye Foundation na ƙasar Saudi Arabia da ta daɗe tana gudanar da kula da masu allurar idanu a jihohin Nijeriya sun koma ƙasar su.
Ita dai Izala Eye Foundation shugaban ta na farko a Jihar Katsina shine marigayi Ahamed Bawa Faskari.
Ana sa ran bayan kammala gyaran asibitin, za ta cigaba da taimakawa al’umma.
