Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Guguwar sauyi ta sauka a Jihar Gombe yayin da jiga-jigan jam’iyyar adawa ta PDP ke cigaba da sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
A makon jiya ne tsohon Manajan Daraktan hukumar tsaro a gwamnatin tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo, Haruna Jonga, ya bar PDP ya koma APC. Yanzu kuma wani jigo a siyasar jihar, Umar Faruk FK, ya fice daga PDP tare da ɗimbin magoya bayansa ya koma APC.
Umar FK ya bayyana cewa ya yi la’akari da halin da PDP ke ciki a jihar Gombe, inda ya tabbatar da cewa jam’iyyar ba za ta kai jama’a ga tudun mun tsira ba.
Ya ce a ganinsa, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na APC shi ne jagoran da zai ci gaba da kai Jihar Gombe ga cigaba da walwala.
Ya yaba da ayyukan raya ƙasa da Gwamna Inuwa ke gudanarwa a fannoni daban-daban, yana mai cewa marar kishin Gombe ne kaɗai ba zai iya ganin ci gaban da ake samu ba.
Ya ƙara da cewa shi da jama’arsa yanzu sun dawo cikin tafiyar Gwamna Inuwa, tare da alƙawarin mara masa baya a burinsa na neman kujerar Sanatan Gombe ta Arewa a shekarar 2027.
Shugaban ƙaramar hukumar Gombe, Barista Sani Ahmad Haruna, ya tarbi Umar FK da magoya bayansa cikin jam’iyyar APC, inda ya tabbatar musu da cewa gwamna ya nuna farin ciki da shigowarsu.
Shi ma shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Gombe, Alhaji Abubakar Danladi, ya bayyana Umar FK a matsayin babban jigo musamman a unguwar Herwagana. Ya ce tun da can yana daga cikin masu ƙalubalantar APC, amma yanzu komawarsa jam’iyyar babbar nasara ce da za ta ƙarfafa APC a yankin.
