Farfesa Yakubu ya yi bankwana da shugabancin INEC

Spread the love

*Shine mafi daɗewa a jagorancin hukumar

*Tinubu ya karrama Yakubu da lambar CON

*Majalisar ƙasa ta amince da Amupitan matsayin sabon shugaba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Tsohon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya sauka daga muƙaminsa tare da miƙa ragamar jagorancin hukumar ga May Agbamuche-Mbu, wacce za ta riƙe muƙamin a matsayin na riƙo kafin naɗa sabon shugaba.

Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin ganawa da kwamishinonin hukumar a hedikwatarta da ke Abuja bayan ya shafe shekarru 10 a kan muƙamin, inda ya kasance shugaban hukumarr zaɓe a Nijeriya mafi daɗewa kan muƙamin a tarihi.

Misis Agbamuche ita ce wacce ta fi dukkan sauran kwamishinonin jimawa a matsayin Babbar Kwamishina a INEC.

Farfesa Yakubu ya kirayi sauran kwamishinoni da daraktoci tare da sauran ma

ma‘aikatan hukumar su bai wa Agbamuche-Mbu cikakken goyon kamar yadda suka ba shi, bayan kafin a naɗa cikakken sabon shugaban hukumar.

A watan Oktoban 2015 tsohon Shugaban ƙasa Marigayi, Muhammadu Buhari ya naɗa Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar INEC, wanda ya maye gurbin Farfesa Attahiru Jega.

Haka kuma ya sake naɗa shi a muƙamin a shekarar 2020 domin cigaba da jagorantar hukumar a karo na biyu.

Farfesa Yakubu ya jagoranci hukumar har na tsawon shekaru 10, inda ja ragamar gudanar da manyan zaɓukan ƙasar a 2019 da 2023.

A gefe guda kuma, sakamakon girmamawa da hidimar da ya ba wa ƙasa a muƙamin, Shugaba Tinubu ya ba shi kyautar girmamawa ta ƙasa ta “Commander of the Order of the Niger’ (CON).

Kakakin Shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata.

A tsawon shekaru goma da ya jagoranci hukumar, Farfesa Yakubu ya jagoranci lamuran manyan zaɓukan 2019 da na 2023, da gabatar da sababbin fasahohi kamar su INEC Result ɓiewing Portal (IReɓ) don inganta gaskiya wajen fitar da sakamako.

A wata takarda da ke ɗauke da 3 ga watan Oktoba, 2025, Farfesa Yakubu ya miƙa godiyarsa ga Shugaba Tinubu akan damar da aka ba shi na shugabantar hukumar har wa’adin biyu.

A nasa ɓangaren, Tinubu ya yaba wa jajircewarsa wajen tabbatar da dimukraɗiyya a ƙasar da kuma gudanar da lamuran zaɓe bisa gaskiya da adalci yayin da yake riƙe da muƙamin.

An haifi Farfesa Mahmood Yakubu a shekarar 1962 a jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabashin Tarayyar Nijeriya kuma ya yi karatunsa ne na firamare a makarantar firamare ta Kobi da ke cikin garin na Bauchi daga bisani kuma sai ya tafi Kwalejin Horas da Malamai da ke garin Toro a jihar ta Bauchi dai inda nan ne ya kammala karatunsa na sakandare. Ta fuskar karatun jami’a kuwa, Farfesa Yakubu ya yi karatunsa na digirin farko a Jami’ar Shehu Usmanu ɗanfodio da ke jihar Sakkwato a Arewa maso gabashin Nijeriya ɗin inda ya karanta ilimin tarihi.

Farfesa Mahmood Yakubu ya kuma yi karatunsa na digiri na biyu a Kwalejin Wolfson da ke Cambridge a Birtaniya inda ya karanci ilimin hulɗa ƙasa da ƙasa inda ya kammala a shekarar 1987. Ya kuma yi digirnsa na uku a a fannin tarihin Nijeriya a Jami’a Oɗford da ke Birtaniya inda ya kammala a shekarar 1991.

Ta fuskar aiki kuwa, Farfesa Mahmood Yakubu ya shafe tsawon lokaci yana koyarwa a Kwalejin Horas da Sojojin Nijeriya da ke Kaduna inda ya ƙware wajen koyar da dabaru na daƙile yaƙin sari-ka-noƙe da kuma abubuwan da suka danganci tarihi da hulɗar ƙasa da ƙasa.

Farfesa Yakubu ya riƙe muƙamin muƙaddashin sakataren kuɗi da mulki na taron ƙasa da aka yi a tarayyar Nijeriya a shekarar 2014, kuma daga bisani wato a watan Oktoban shekarar 2015 ne Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya naɗa shi a matsayin shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta wato INEC.

Muna son a kafa kwamitin da zai zaɓi sabon Shugaban INEC – Jam’iyyun siyasa

Jam’iyyun siyasa a Nijeriya sun fara martani kan saukar shugaban hukumar zaɓen, Farfesa Mahmood Yakubu daga muƙaminsa bayan kawo karshen wa’adinsa na biyu.

Kwamitin tuntuɓa tsakanin jam’iyyun Nijeriya ya yi kiran samar da wani kwamitin da zai jagoranci naɗa sabon shugaban hukumar da kuma kwamishinoni.

Shugaban ƙasa ne kundin tsarin mulki ya ba damar zaɓen shugaban hukumar zaɓe bayan tuntuɓar majalisar ƙasa da ta ƙunshi tsoffin shugabanni da gwamnoni da shugabanannin majalisun tarayya.

Gamayyar jam’iyyun siyasar na Nijeriya ya ce idan har ana son tabbatar da hukumar zaɓen a matsayin mai ‘yanci kuma mai zaman kanta da kuma tabbatar da tsabtar tsarin zaɓe, akwai buƙatar sake tsarin zaɓen shugabannin hukumar.

Jam’iyyun siyasar sun ce akwai buƙatar samar da kwamiti na musamman mai zaman kansa wanda zai ƙunshi wakilan jam’iyyun siyasa da na ƙungiyoyin fararen hula da kuma kwamitin majalisun tarayya wanda za a ɗora wa alhakin zaɓen sabon shugaban hukumar INEC.

“Shugaban ƙasa ne yake naɗa shugaban INEC da kwamishinoni, kuma shugaban ƙasa shi ma ɗan takara ne, don haka idan har ana son zaɓe ya tafi yadda ya kamata, dole sai an canza yadda ake naɗa masu kula da aikin zaɓe,” inji Injiniya Yabagi Sani Shugaban J’am’iyyar ADP kuma tsohon shugaban ƙungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa ta IPAC.

Ya ƙara da cewa, ya kamata a ce idan har za a zaɓi sabon shugaban zaɓe a tallata ga masu buƙata su nema.

“Idan aka yi talla, waɗanda suka nuna suna so kuma aka tace daga nan sai a miƙa sunayensu ga majalisa,” inji Yabagi Sani.

Jam’iyyun siyasar dai na ganin idan har aka samar da wakilci daga ɓangarori da dama wajen zaɓen shugaban INEC zai dawo wa hukumar zaɓen da martaba da darajarta.

Sun kuma buƙaci a samar da hukuma ta musamman da za ta hukunta masu laifin zaɓe, suna masu cewa yin hakan zai rage laifukan da ake aikata lokacin zaɓe musamman sayen ƙuri’u da satar ƙuri’a da kuma maguɗi.

Majalisar ƙasa ta amince da naɗin Amupitan a matsayin sabon Shugaban INEC:

Majalisar magabata ta amince da naɗin Farfesa Joash Ojo Amupitan (SAN) daga yankin Arewa ta Tsakiya a matsayin sabon Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC).

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gabatar da Amupitan a matsayin wanda zai cike gurbin Farfesa Mahmood Yakubu, wanda ya sauka daga kujerar a ranar Talata bayan ƙarewar wa’adinsa. Yakubu ya yi aiki daga 2015 zuwa Oktoba 2025.

Shugaba Tinubu ya shaida wa majalisar cewa Amupitan shi ne mutum na farko da ya fito daga jihar Kogi a Arewa ta Tsakiya da aka zaɓa domin ya riƙe wannan muƙami kuma ba ya siyasa.

Mambobin majalisar dai sun amince da naɗin, inda Gwamna Ahmed Usman Ododo ya bayyana Amupitan a matsayin mutum mai gaskiya.

Dangane da kundin tsarin mulki, yanzu Shugaba Tinubu zai aika da sunan Amupitan zuwa majalisar dattawa domin tantancewa.

Amupitan, mai shekaru 58, daga Ayetoro Gbede, ƙaramar Hukumar Ijumu a jihar Kogi, Farfesa ne a fannin shari’a a Jami’ar Jos, Filato. Shi ma tsohon ɗalibin jami’ar ne.

Ya ƙware a fannin Dokar Kamfani, Dokar Shaida, Gudanar da Kamfanoni da Dokar Sirri. Ya zama Babban Lauyan Nijeriya (SAN) a watan Satumba 2014.

An haifi Amupitan a ranar 25 ga Afrilu, 1967.

Bayan kammala karatun firamare da sakandire, ya halarci Kwara Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kwara, Ilorin, daga 1982 zuwa 1984, da Jami’ar Jos daga 1984 zuwa 1987. Ya zama ƙwararren lauya a shekarar 1988.

Ya samu digirgir a fannin shari’a (LLM) a Jami’ar Jos a shekarar 1993, sannan ya yi digirin digirgir a shekarar 2007, a cikin karatunsa na ilimi da ya fara a shekarar 1989, bayan ya yi hidimar ƙasa NYSC a kamfanin buga littattafai na jihar Bauchi da ke Bauchi daga 1988 zuwa 1989.

A yanzu haka yana matsayin Mataimakin Shugaban Jami’ar Jos (Administration) a Jami’ar Jos, muƙamin da yake riƙe da shi tare da zama Pro-Chancellor kuma Shugaban Majalisar Gudanarwa na Jami’ar Joseph Ayo Babalola da ke Jihar Osun.

Daga cikin muƙaman ilimi da ya riƙe a Jami’ar Jos akwai: Shugaban Kwamitin Deans da Daraktoci (2012-2014); Shugaban Kwalejin Shari’a (2008-2014); da Shugaban Dokar Jama’a (2006-2008).

Ban da ɓangaren ilimi kuma, Amupitan yana aiki a matsayin memba na hukumar Integrated Dairies Limited a ɓom, memba na Cibiyar Gudanar da Nazarin Shari’a ta Nijeriya, kuma memba na Majalisar Ilimin Shari’a (2008-2014), a tsakanin sauran ayyuka. Ya kasance mamba a hukumar Riss Oil Limited, Abuja (1996-2004).

Amupitan ya rubuta litattafai da dama akan doka, kamar, Corporate Goɓernance: Models and Principles(2008); Documentary Eɓidence in Nigeria (2008); Eɓidence Law: Theory and Practice in Nigeria(2013), Principles of Company Law(2013) and an Introduction to the Law of Trust in Nigeria (2014).

Yana da aure da ’ya’ya huɗu.

By ukarofi