EFCC ta kafa bincike kan shugaban NAHCON

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta ƙasa (EFCC), ta kama kuma ta fara bincikar shugaban Hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, bisa zargin al’amuran almundahana da suka haura biliyoyin naira.

Majiyoyi daga EFCC sun bayyana cewa Farfesa Pakistan ya isa hedikwatar hukumar da ke Abuja ne da misalin ƙarfe 12 na rana, ranar Talata.

Wata majiya ta ƙara tabbatar da cewa shugaban hukumar alhazai ya isa tare da lauyansa na kashin ƙai, Kazeem Atetebi.

An kuma ce, bayan an kammala tambayoyi na farko, an ba shi beli, tare da umartar shi da ya riƙa komawa ofishin EFCC kowace rana da ƙarfe 10 na safe har sai an kammala bincike.

A cewar wani jami’in da ke da masaniya kan binciken, an gano cewa Farfesa Pakistan ya wuce kasafin kuɗin aikin Hajjin shekarar 2025 da kashi 300 cikin 100.

“Fadar shugaban ƙasa ta amince da kasafin kuɗin dala miliyan 14 kacal — inda 70% za ta fito daga kuɗaɗen shiga na NAHCON, sannan 30% daga gwamnatin tarayya.

Amma Farfesa Pakistan ya kashe fiye da dala miliyan 48 a aikin Hajjin 2025 ba tare da izini ba,” inji majiyar EFCC.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa hukumar EFCC ta riga ta yi wa ma’aikatan NAHCON sama da 20 tambayoyi, kuma mafi yawansu sun nuna yatsansu ga shugaban hukumar a matsayin wanda ke da hannu a lamarin.

Daga cikin batutuwan da ake bincike a kansa akwai: Naira biliyan 25 da aka ce an kashe kan ƙarin gadon masaukai a Mashaa’ir, Naira biliyan 1.6 da aka ce an ware don matan ma’aikata, Naira biliyan 8 don gadon masaukin gaggawa a Makkah, da kuma biyan kuɗaɗe da suka zarce kasafin shekara da sama da kashi 300%.

Haka kuma, akwai biliyan 25 da aka kashe a kan jami’ai, ma’aikata da mambobin kwamitin hukumar, da kuma biliyan 1.4 a matsayin kuɗin alawus na kwamitoci.

An kuma bayyana cewa adadin gadon masaukin Madinah ya tashi daga 11,000 zuwa 18,000 domin alhazai 41,000, abin da ake ganin ya haifar da rikicewar lissafi da rashin gaskiya a kashe kuɗi.

Rahotanni sun nuna cewa an shirya shugaban hukumar alhazai ya bayyana gaban EFCC tun ranar Laraba, 17 ga Satumba 2025, amma ya nemi a ɗage zaman domin tafiya Saudiyya, don haka aka sake tsayar da ranar 2 ga Oktoba 2025.

Sai dai, duk da cewa ya dawo daga tafiya, bai bayyana a ranar da aka tsara ba.

Wani jami’in tsaro daga fadar shugaban ƙasa ya ce Farfesa Pakistan ya halarci taron da mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, tare da wasu jami’an NAHCON a ranar 6 ga Oktoba 2025, inda Shettima ya umarci hukumar da ta rage farashin kujerar aikin Hajji na 2026.

By ukarofi