Cika shekara 60: Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta nemi haɗa hannu da Blueprint

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar marubuta labarin wasanni ta ƙasa (SWAN) ta yi kira ga jaridar Blueprint da ta haɗa hannu da ita gami da tallafa mata wajen jagorantar wasu al’amura a yayin da take bikin cika shekaru 60 da kafuwa.

Za a gudanar da bikin ne a daga ranar 29 zuwa 31 ga watan nan na Oktoba, 2025 a Abuja.

Sakataren SWAN Mista Ikenna Okonkwo, wanda shi ne ya jagoranci tawagar kwamitin bikin da wasu mambobin ƙungiyar zuwa gidan jaridar, ya ce damawa da gidajen jaridu abu ne muhimmanci ga taron.

Ya bayyana Blueprint a matsayin gidan jarida mai ƙoƙarin tsage gaskiya da kishin ƙasa musamman wajen faɗaɗa aikin jaridar wasanni da haɗin kan ƙasa.

Okonkwo ya bayyana cewa, taron wanda za a gudanar a ƙarshen Oktoba zai ƙunshi lakca ta ƙasa, addu’o’i daga wakilan addinai, taron raba kyautuka da kuma karrama wasu tsofaffin ƴan jarida.

A nasa jawabin, Darakta Manaja kuma Shugaban Blueprint, Mallam Salisu Umar ya yaba wa SWAN bisa yadda take nuna ƙwarewa da sadaukarwa wajen aikin jaridar harkar wasanni a kowane matakai.

Ya kuma ce, sun gamsu da nasarorin da ƙungiyar take samu don haka Blueprint za ta haɗa hannu da ita wajen inganta ci-gaban wasanni da haɗin kan al’umma.

Kazalika, ya bayyana farin cikinsa a madadin gidan jaridar bisa yadda Babban Editan Blueprint, Mista Clem Oluwole, ya shiga sahun waɗanda za a karrama a bikin.

By Babaji