Tinubu ya yafe wa Mamman Vatsa, Herbert Macaulay, Faruk Lawan da wasu 173

Spread the love

Shugaba Bola Tinubu, ya yi amfani da ikonsa na gafarar shugaban ƙasa wajen yafe wa fitattun mutane da dama ciki har da Herbert Macaulay da Manjo Janar Mamman Jiya Vatsa wanda aka kashe a 1986 bisa tuhumar yunƙurin juyin mulki.

Mamman Vatsa, wanda kuma shahararren mawaƙin zube ne, ya samu gafarar ne bayan amincewar Majalisar Ƙasa a yayin wani zama a Abuja, ranar Alhamis.

Haka kuma, shugaban ƙasa ya yafe wa Herbert Macaulay, wato ɗaya daga cikin jagororin neman ƴancin Nijeriya da ya kafa jam’iyyar NCNC tare da Dakta Nnamdi Azikiwe.

Duk da Macaulay ya rasu tun a 1946, har yanzu yana ɗauke da tabon kasancewa ɗan gidan yari daga hukuncin da Turawan mulkin mallaka suka yanke masa.

Tinubu ya kuma yafe wa wasu tsofaffin masu laifi, ciki har da tsohon ɗan majalisa Farouk Lawan, tare da Mrs Anastasia Daniel Nwaobia, Barista Hussaini Umar, da Ayinla Saadu Alanamu. An bayyana cewa sun nuna nadama kuma ana son ba su damar sake shiga cikin al’umma.

Sauran da suka ci gajiyar gafarar sun haɗa da Nweke Francis Chibueze, wanda akai wa daurin rai-da-rai kan laifin hodar iblis, da kuma Dr Nwogu Peters wanda ya shafe shekaru 12 cikin hukuncin shekara 17 kan zamba.

Haka zalika, shugaban ƙasar ya bai wa Ogoni Nine cikakkiyar gafara, waɗanda suka haɗa da Ken Saro-Wiwa, Saturday Dobee, Nordu Eawo, Daniel Gbooko, Paul Levera, Felix Nuate, Baribor Bera, Barinem Kiobel da John Kpuine.

Ya kuma ba da lambar girmamawa ta ƙasa ga Ogoni Four, Cif Albert Badey, Cif Edward Kobani, Cif Samuel Orage da Theophilus Orage.

An bai wa fursunoni 82 cikakkiyar gafara, an rage wa 65 hukunci, sannan an sauya wa 7 girman hukuncin daga hukuncin kisa zuwa daurin rai-da-rai.

Shugaban ya yi wannan ne bisa shawarwarin Kwamitin Taimaka wa Shugaban Ƙasa kan Gafara (PACPM) wanda Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN), ke jagoranta. Kwamitin ya kunshi mambobi 12 ciki har da wakilan hukumar ’yan sanda, hukumar gyaran hali, hukumar kare haƙƙin bil’adama, majalisar koli ta musulunci da kuma majalisar kiristoci ta Najeriya.

Rahoton kwamitin ya nuna cewa daga cikin 294 da aka tantance, mutum 175 aka amince su ci gajiyar wannan shirin bisa ƙa’idoji kamar tsufa, rashin lafiya, ƙarancin shekaru, da kyakkyawan halayya a gidan gyaran hali.

By Babaji