Sanusi Sami ya zama sabon Sarkin Zuru 

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya amince da naɗin Alhaji Sanusi Mika’ilu Sami a matsayin sabon Sarkin Zuru.

Naɗin nasa ya biyo bayan rasuwar tsohon Sarki Muhammad Sani Sami Gomo II, wanda ya rasu a ranar 16 ga Agusta, 2025, a wani asibitin Landon.

Yayin da ya ke gabatar da takardar naɗin ga sabon sarkin jiya Alhamis a garin Zuru, Kwamishinan ƙananan Hukumomi da Masarautu na Jihar Kebbi, Alhaji Garba Dutsin-Mari, ya ce, naɗin ya biyo bayan shawarar kwamitin zaɓen.

Dutsin-Mari ya ce daga cikin ‘yan takara uku da suka nemi wannan muƙami da kwamitin zaɓen masarautar Zuru ya tantance, Sanusi Mika’ilu Sami ya samu ƙuri’u mafi rinjaye da ya hau kan karagar mulki.

Ya gode wa gwamnan jihar Kebbi bisa amincewa da naɗin sabon sarkin, sannan ya buƙaci sabon sarkin da ya tabbatar da amincewar da aka yi masa.

Kwamishinan ya shawarci sabon sarkin da ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa bisa tsoron Allah.

A halin da ake ciki, Gwamna Idris ya bayyana cewa babu wani jami’in da ya yi aiki a ƙarƙashin tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ke da hurumin sukar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu kan harkokin tsaro, yana mai jaddada cewa an gaji ƙalubalen.

Gwamnan ya bayyana haka ne a yayin wani addu’a ta musamman da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi domin tunawa da cika shekaru 34 da kafuwar Jihar Kebbi a ranar Laraba.

Gwamna Idris ya bayyana cewa ƙalubalen tsaro ya riga ya samu kafin gwamnati mai ci yanzu inda ya ce a duk lokacin da jiharsa ta fuskanci wani rikici, gwamnatin tarayya ta kan yi gaggawar mayar da martani.

“Lokacin da al’amuran tsaro suka taso a kudancin Kebbi, na tuntuɓi babban hafsan hafsoshin tsaron ƙasar, na buƙaci gwamnatin tarayya ta shiga tsakani, inda ta mayar da martani, CDS ta tura dakaru 10 masu sulke, waɗanda aka rarraba a yankunan da abin ya shafa,’ inji shi.

Gwamnan ya kuma soki wasu ’yan siyasa mazauna Abuja da ke zaune a Kebbi kan sanya siyasa a ƙoƙarin gwamnati kan batun tsaro.

By ukarofi