
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Makarantu da asibitoci da dama aka gyara a sassan Ƙaramar Hukumar Bichi da ke Kano a yunƙurin gwamnatin jihar ƙarƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na bunƙasa harkokin illimi da lafiyar al’umma.
Shugaban Majalisar Ƙaramar Hukumar, Alhaji Hamza Sule Mai Fata ya bayyana haka a lokacin da yake karɓar manyan jami’an Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma a wata ziyara da suka kai yankin, kamar yadda jami’ar yaɗa labaran ƙaramar hukumar, Jamila Abdullahi R/Lemo ta bayyana.
Sule Mai Fata ya ce, Bichi ta samu nasarar gyaran makarantu da asibitoci masu yawa tare da samar da kayan koyo da koyarwa da kuma sauran kayan aiki da ake buƙata a asibitocin da aka gyara.
Ya kuma bayyana cewa dukkan mazaɓu 11 na fadin yankin sun amfana da gyaran makarantu biyu zuwa uku bisa sahalewar gwamnatin jiha ta hanyar kulawar kansilan kowace mazaba tare kuma da sake gyaran makarantu 33 a fadin karamar hukumar.
Shugaban yankin, ya kara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya umarci kowane shugaban ƙaramar hukuma daga kananan hukumomi 44 dake jihar nan, ya rubuto dukkan makarantun da suka lalace a karamar hukumarsa domin tabbatar da cewar an gyara su kamar yadda yakamata a yi musu gyara.
Ya ce, daga cikin asibitocin da Majalisar karamar hukumar ta gyara sun hadar da; asibitocin garuruwan Damargu da Kwamarawa da Tudun-Wulli, yayin da kuma akwai asibitoci hudu da ake aikin gyaransu a halin yanzu.
“Asibitoci ana ta yi, idan ka je Tudun-Wulli za ka ga yadda aka mayar da shi katafare babba kamar ma yafi na wata jihar, za kuma a sa masa sola.” In ji shi.
Tun da farko a jawabinsa, Kwamishinan Ma’aikatar Raya Karkara da Cigaban Al’umma, Alhaji Abdulkadir Abdus-Salam, wanda Babban Sakataren Ma’aikatar, Alhaji Musbahu Badawi Maigari, ya wakilta, ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya ummarce su su ziyarci sassan kananan hukumomin jihar domin su gana da Dagatai da masu unguwanni da sauran shugabanin al’umma, domin sanin irin matsalolin da suke ciki da kuma bukatar da suke da ita daga bangaren gwamnati tare da bai wa gwamnati damar sanin halin da jama’arta ke ciki.
“Tun da muka fara Bichi ita ce karamar hukuma ta ashirin da uku (23), Alhamdu lilLahi. Duk inda muka je muna fadakar da su a kan wannan kudiri na Gwamna, kuma kudiri ne da zai taimaka wa jama’ar Kano tun daga kasa; su fadi bukatunsu gwamnati ta rika dauka daya bayan daya tana musu maganin wadannan matsalolin nasu.” In ji shi.
A nasa jawabin, Hakimin Bichi Galadima Kano Alhaji Mannir Sanusi, ya yi jawabi mai tsawo a kan irin ayyukan cigaba da Mai Martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammad Sanusi na biyu ya aiwatar da ayyukan alheri wadanda Suka shafi rayuwar al’ummarsa tare da tabbatar da kare darajar jama arsa da kuma tabbaar da adalci a tsakanin su.
Taron ya samu halartar Dagatai da masu unguwanni da limaman Karamar Hukumar Bichi.





