Ministan yaɗa labarai Idris ya yi kira da a ƙara ba da goyon baya ga shugaba Tinubu don ciyar da Nijeriya a gaba

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a na ƙasa Alh. Muhammed Idris ya jaddada buƙatar samun ƙarin goyon baya daga ‘yan Najeriya ga gwamnatin tarayya don ba ta damar cimma sabon burinta na samar da ingantacciyar ƙasa da cigaban ta.

Ya yi wannan kiran ne a jawabin maraba a wajen wani gangamin wayar da kan jama’a kan rahoton cigaban da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu yayi a tsakiyar mulkin sa a yankin Arewa maso Yamma da aka gudanar a otal ɗin City King da ke Gusau ranar Alhamis.

Ministan wanda ya samu wakilcin Auwal Balarabe, shugaban ma’aikatar yaɗa labarai da wayar da kan jama’a ta ƙasa reshen Jihar Zamfara, ya bayyana cewa wayar da kan jama’a zai bawa ‘yan Nijeriya dama su san ayyukan raya ƙasa daban-daban da wannan gwamnati ke aiwatarwa a ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ministan ya bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya taka rawar gani a wasu ɓangarori na tattalin arziki kamar inganta tsaro, samar da ababen more rayuwa, noma, ilimi, samar da ruwa, makamashi, haɓaka tattalin arziki da harkokin zamantakewa gami da inganta ƙasa Najeriya .

“A wannan karon ma’aikatar ta fara gangamin wayar da kan al’ummar Nijeriya baki ɗaya kan wa’adin rahoton gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a ƙarƙashin shirinsa na Renewed Hope”.

Ministan ya ce, an samar da wani muhimmin mataki inda sama da 300,000 suka ci gajiyar shirin ba da lamuni na ɗalibai “NELFUND”, da Kuma mutum 900,000 suka ci gajiyar shirin lamuni na shugaban ƙasa.

A cewarsa, sama da ayyukan gina tituna 440 gwamnati mai ci ta bayar a faɗin ƙasar nan.

Dokta Mohammed Idris ya kuma ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta fara biyan mafi ƙarancin albashi na N70,000, da kuma bunƙasa sauran tallafin noma, samar da ababen more rayuwa da sauran ayyukan gwamnatin tarayya na rage wahalhalun da ‘yan Najeriya ke ciki.

“Don haka ina kira ga mutanen Zamfara da su yi amfani da ayyukan raya ƙasa don cin moriyar dimokuraɗiyya tare da marawa gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a ƙoƙarin ta na kawo sauyi ingantacce”. Idris ya ce

A nasa jawabin shugaban jam’iyyar APC na jiha Alh. Tukur Danfulani wanda ya samu wakilcin mataimakin sakataren walwala na Jam’iyyar, Alh. Shehu ya yabawa gwamnatin tarayya ƙarƙashin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu kan ƙoƙarin ta na magance matsalar rashin tsaro a jihar.

By ukarofi