Tinubu ya yi dirar mikiya kan almundahanar kurkuku

Spread the love

*An kori jami’ai 15 tare da hukunta 59

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kori jami’ai 15 na Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta ƙasa (NCoS) tare da rage matsayin wasu 59 saboda aikata laifuka da rashin ɗa’a a wuraren aiki daban-daban.

Wannan na cikin sanarwar da Hukumar CDCFIB, Mai Kula da Harkokin Hukumomin Sibil Defens, Gudajen Gyaran Hali, Kashe Gobara da Shige da Fice ta fitar ne.

Sanarwar ta ce, an ɗauki wannan matakin ne bayan nazari kan hukuncin ladabtarwa da suka shafi jami’an hukumar daga sassa daban-daban na ƙasar.

A cewar Umar Abubakar, jami’in hulɗa da jama’a na NCoS, hukuncin ya biyo bayan shawarwarin da kwamitin ladabtarwa da manyan ayyuka (BDGPC) ya bayar, bayan bincike mai zurfi.

Ya ce, wannan mataki ya ƙara nuna ƙudurin Gwamnatin Tarayya na tabbatar da ɗa’a da biyayya a cikin Hukumar Kula da Gidajen Yari. 

“Bayan cikakken nazari da dubawa, hukumar ta amince da ɗaukar matakan ladabtarwa daban-daban domin tabbatar da ɗa’a da kiyaye mutuncinta.

“An kori ma’aikata 15 gabaɗaya saboda manyan laifuka da karya ƙa’idar aiki. An rage matsayin ma’aikata 59 matsayi saboda tabbatar da saɓawa ƙa’idar aiki da rashin ɗa’a. Sannan an tura wasiƙun gargaɗi ga ma’aikata 42,” inji Umar Abubakar.

Har ila yau, Umar Abubakar ya ce an wanke ma’aikata 16 daga zarge-zargen da ake musu, yayin da wasu bakwai ke kan dakatarwa domin tantance hannunsu a wani laifi da ake bincike.

Umar ya ƙara da cewa, “Bayan haka an dakatar da jami’i daga aiki tare da bayar da umarni a miƙa shi ga Hukumar EFCC domin gurfanar da shi a gaban kotu saboda girman laifin da ya aikata.

“Ma’aikata 8 an tilasta musu yin ritaya yayin da aka dawo da jami’i ɗaya kan tsohon matsayinsa, tare da umarnin ya mayar da albashin da ya karɓa lokacin da yake riƙe da sabon matsayin da ya samu ba bisa ƙa’ida ba.

A ƙarshe, Umar ya ce, hukumar CDCFIB, ƙarƙashin Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, na nan kan bakarta na tabbatar da bin ƙa’idoji a tsakanin ma’aikata.

By ukarofi