Yawancin rukunin gidajen da aka yi watsi da su a Abuja na ma’aikatan gwamnati ne, inji Shugaban EFCC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC, ta ce bincikenta ya nuna cewa da dama daga cikin rukunin gidaje da aka bar su kara zube a Birnin Tarayya Abuja na ma’aikatan gwamnati ne.

Da ya ke magana ranar Laraba a Abuja yayin taron tattaunawa akan harkokin tsare-tsare, Shugaban hukumar, Ola Olukoyede ya ce nan ba da jimawa ba tawaga ta musamman daga gare su za ta fara ziyartar ire-iren kadarorin waɗanda wasun su an jingine su tsawon sama da shekaru goma.

Ya gargaɗi lauyoyi da dillalan harkokin cigaban rukunin gidaje da kada su bari waɗanda suka yi almundahana ga dukiyar ƙasa su yi amfani da su wajen cimma manufofinsu.

Ya kuma ce, tawagar da suka samar za ta yi aiki ne a Abuja da sauran jihohin Nijeriya domin gano masu mallakar gidajen.

Olukoyede ya bayyana cewa, “zai baka mamaki a ce wasu daga cikin waɗannan rukunin gidajen an bar su kara zube na tsawon shekaru 10 zuwa 20. Kawai sun kai shi wani mataki, sannan sai suka jingine shi. Ba wanda ya san abinda ke tafiya.”

Ya ƙara da cewa, daga cikin bincikensu sun gano cewa da dama daga cikin rukunin gidajen, ma’aikatan gwamnati da suka saci kuɗaɗe ne suke gina su.

By Babaji