
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Sanata a Majalisar Dattawan Nijeriya, Ibrahim Musa Kontagora ya rasu a Abuja bayan fama da rashin lafiya.
Marigayin ya rasu a ranar Alhamis, 7 ga watan Agusta, 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne a Asibitin Nizamiye da ke birnin tarayyar bayan ma’aikatan asibitin sun ƙi yi masa aiki, saboda kasa biyan Dala cikon 15,000, wato Naira miliyan 22.9 akan lokaci.
Asibitin ya gabatar wa tsohon sanatan, wanda ya wakilci mazaɓar Neja ta Arewa daga 2011 zuwa 2015 a majalisar kuɗin aiki da adadinsu ya kai kimanin Dala 30,000 inda kaɗai abinda ya iya biya shi ine rabinsa.
Jami’an asibitin sun ce za su yi masa aiki ne a lokacin da aka biya sauran kuɗin, inda iyalansa suka yi ƙoƙarin samo cikon, saidai sun makara domin a lokacin da suka zo biyan sun tarar ya riga ya cika, kamar yadda ɗaya daga cikin su ya shaida wa manema labarai.
Wani da ya yi magana da yawun iyalan ya ce asibitin yana da tsarin karɓar kuɗin aiki kafin fara magani, don haka ba za a ɗora masa alhakin rashin ba.
Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago yana ɗaya daga cikin ƴan siyasar da suka bada gudumawar kuɗin aikin, da Sanata Aliyu Abdullahi, waɗanda duk sun miƙa ta’aziyyarsu ga iyalan mamacin.
Marigayin ɗan siyasar ya rayu da mata ɗaya da ƴaƴa, sannan an yi masa jana’iza a babban masallacin ƙasa, wato National Mosque da ke Abuja da misalin ƙarfe 4 na yammacin ranar.
